Ministan da aka nada a ma’aikatar jin kai da yaki da fatara, Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa kusan kashi 65 cikin 100 na talakawa na zaune ne a yankin arewacin Nijeriya, don haka, yankin ya cancanci karin kaso bisa la’akari da bukatun gaggawa.
Yilwatda ya bayyana hakan ne a yayin da yake jawabi a gaban Sanatoci domin tantance shi a matsayin minista kuma mamba a majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) a ranar Laraba.
- CMSA: An Yi Nasarar Harba Kumbon Shenzhou-19 Mai Dakon ’Yan Sama Jannati
- Tinubu Ya Bayar Da Umarnin Gyara Wutar Lantarkin Arewa Cikin Gaggawa
Da yake magana kan hanyoyin da ya kamata a bi domin rage radadin talauci a Nijeriya, Yilwatda ya ce, “kashi 65 na talakawa suna zaune a Arewa yayin da kashi 35 ke zaune a Kudu, ya kamata, mu yi la’akari da abunda ake bukata a kowace karamar hukuma da jihohi, ta yadda za a raba kudaden shiga duba da jihar da tafi bukata.”
Daga nan aka nemi Yilwatda, ya yi gaisuwa ya tafi, an sallame shi.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ne ya zabi Yilwatda a makon da ya gabata domin ya maye gurbin Betta Edu da aka dakatar kuma daga baya aka sallame ta a matsayin ministar harkokin jin kai da rage radadin talauci.