Kasar Argentina ta gayyaci Lionel Messi domin buga mata wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a Kudancin Amurka duk da cewa yana cikin jerin wadanda suka ji rauni a kungiyarsa ta Inter Miami.
Messi bai buga wasan da kungiyarsa ta sha kashi a hannun Chicago da ci 4-1 a ranar Laraba ba sakamakon jinya da yake yi.
- Messi, Osimhen, Haaland Suna Cikin ‘Yan Wasan Da Ke Takarar “FIFA The Best”
- Yadda Barakar PSG Ta Sake Fitowa Fili
Ya buga wa kungiyar wasa na tsawon mintuna 37 ne kacal ya samu rauni tun ranar 3 ga Satumba.
A ranar 12 ga watan Oktoba ne Argentina za ta karbi bakuncin Paraguay sannan kuma za ta kara da Peru kwanaki biyar a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta 2026 CONMEBOL.
Dan wasan mai shekaru 36 bai buga wasanni uku na karshe na Inter Miami ba sannan kuma babu wani cikakken bayani game da lafiyarsa ba.