Tawagar kasar Argentina ta koma ta daya a kan jadawalin kasashen da ke kan gaba a buga kwallon kafa a duniya da FIFA ta sanar kuma wannan shi ne karo na farko da Argentina ta hau kan wannan matakin tun bayan shekara shida, wadda ta lashe kofin duniya a Katar a 2022.
Kasar ta Argentina ta samu wannan ci gaban bayan nasara biyu a wasan sada zumunta da ta ci Panama da Curacao, ita kuwa Brazil rashin nasara ta yi a hannun Morocco.
- Sallah: Gwamna Bagudu Ya Umarci A Biya Albashin Watan Afrilu
- INEC Ta Raba Muhimman Kayyayakin Zabe Don Kammala Zaben Gwamnan Kebbi
Faransa, wadda ta doke Netherlands da Jamhuriyar Ireland a wasannin neman shiga Euro 2024 ta koma ta biyu sai Brazil wadda take matakin farko ta koma ta uku, Ingila wadda ta ci Italiya da Ukraine tana ta biyar da Sifaniya a jerin ‘yan 10 farko.
Ga Jerin goman farko a FIFA
1 Argentina Argentina 2 France 3 Brazil 4 Belgium 5 England 6 Netherlands 7 Croatia
8 Italy 9 Portugal 10 Spain.
Daga nan nahiyar Afirka kuma tawagar ‘yan wasan Super Eagles ta Nigeriya wadda Jose Pesseiro ke jan ragama ta yi kasa ajadawlin kungiyoyin da ke kan gaba a iya kwallo a duniya.
Najeriya wadda ta je ta ci Guinea Bissau 1-0 a watan jiya a wasan cikin rukuni a neman shiga kofin Afirka tana ta 40 a duniya, wadda take ta 35 a Disamba sannan a nahiyar Afirka kuwa Super Eagles wadda take ta biyar a baya yanzu Masar ta karbi gurbin, NIjeriya ta yi kasa zuwa ta shida.
Ita ma Kamaru ta yi kasa daga mataki na hudu a baya yanzu tana ta bakwai a Afirka wanda hakan yake nufin akwai aiki sosai a gaban manya-manyan kasashen Afirka musamman masu tasiri a kwallon kafa.
Ga Jerin 10 na farko a Afirka
Morocco 2. Senegal 3. Tunisia. 4. Algeria 5. Masar 6. Najeriya 7. Kamaru 8 Ibory Coast
9.Burkina Faso 10. Mali.