Ko da yake Arsenal da PSG sun saba lashe kofuna a gida, amma har yanzu babu wani a cikinsu da ya taɓa ɗaukar kofin Gasar Zakarun Turai.
Arsenal dai ta shafe fiye da shekaru 20 ba tare da lashe gasar Firimiya ba, sai dai bayan Liverpool da Manchester United, babu wata ƙungiya a Ingila da ta fi Arsenal yawan kofuna.
- Nijeriya Na Ke Yi Wa Biyayya Ba Wani Ko Jam’iyya Ba – El-Rufai
- ‘Yan Ta’adda Sun Hallaka Mutum 8 Da Bam A Borno
PSG ma kamar Arsenal, ta ci kofuna da dama tun bayan zuwan masu hannun jari daga Qatar.
Yanzu haka, ƙungiyoyin biyu za su kara yau a filin Emirates da ke Landan domin wasan kusa da na ƙarshe na Gasar Zakarun Turai.
Duk da sun taɓa zuwa wasan ƙarshe na wannan gasa a wasu lokuta daban-daban, babu ɗayansu da ya samu nasara.
Wannan ya sa wasan yau zai zama mai ɗaukar hankali, domin kowanne daga cikinsu na burin ɗaukar kofin a karo na farko, domin a dakatar da yawan dariyar da ‘yan adawa ke musu.
A zagayen rukuni da suka haɗu a farkon wannan kakar, Arsenal ta lallasa PSG da ci 2-0.
Kocin Arsenal yanzu, Mikel Arteta, ya taɓa buga wasa a duka ƙungiyoyin.
Yana fatan ya zama kocin farko da zai jagoranci Arsenal ta lashe kofin Zakarun Turai.
Wannan ya sa magoya bayan Arsenal ke fatan ganin ƙungiyarsu ta yi abin mamaki a wasan da za a fara da misalin ƙarfe 8 na dare agogon Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp