Arsenal ta kammala ɗaukar Martin Zubimendi daga Real Sociedad a kan kusan fam miliyan 60, inda ɗan wasan tsakiyar Sifaniya ya zama ɗan wasa na biyu da Gunners ta saya a kasuwar bana, bayan zuwan mai tsaron raga Kepa Arrizabalaga daga Chelsea. Zubimendi ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru biyar a Emirates, kuma zai saka lamba 36 a ƙungiyar.
Ɗan wasan mai shekaru 26 ya ƙi amincewa da tayin Liverpool a bazarar da ta gabata, amma ya zaɓi Arsenal saboda salon wasan ƙungiyar ya dace da shi. Ya ce burinsa shi ne taimakawa Arsenal wajen lashe manyan kofuna, kuma Mikel Arteta da abokin wasansa Merino sun taka rawa wajen shawo kansa zuwa kungiyar.
- Ana Tuhumar Tsohon Ɗan Wasan Arsenal Thomas Partey Da Laifin Fyaɗe A Ƙasar Ingila
- PSG Ta Yi Waje Rod Da Arsenal A Gasar Zakarun Turai
Zubimendi ya taka leda sau 236 a Real Sociedad, inda ya jefa ƙwallaye 10 kafin sauya sheka. Shi ne dan wasa na biyu da Arsenal ta ɗauko daga Sociedad cikin ɗan lokaci bayan zuwan Merino a bara.
A matakin ƙasa, Zubimendi ya taimaka wa Sifaniya lashe gasar Euro 2024, inda ya canji Rodri a wasan ƙarshe da Ingila. Ya buga wa ƙasar wasanni 19, kuma ya zura ƙwallo a ragar Portugal a gasar Uefa Nations League kafin Spain ta sha kashi a bugun fenareti.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp