Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta lallasa abokiyar karawarta Manchester United da ci 3 da 1.
Marcus Rashford ne ya fara jefa kwallo a ragar Arsenal a minti na 27 kafin Martin Ordeegard ya farke kwallon miniti daya tsakani.
Wasan na kunnen doki kafin sabon dan wasan Arsenal Declan Rice ya jefa wa Arsenal kwallo ana gab da tashi wasan.
A minti na 97 bayan karin lokaci tsohon dan wasan Manchester City Gabriel Jesus ya jefa kwallonsa ta farko a wannan kakar wasa ta bana.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp