Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta yi rashin nasara a karon farko a duka wasannin da ta buga a bana.
Arsenal wadda ke matsayi na uku a gasar Firimiyar Ingila ta yi rashin nasara a hannun Lens ta kasar Faransa da ci 2 da 1 a gasar UEFA Champions League da suka buga a ranar Talata.
- Akwai Yiwuwar Kara Mafi Karancin Albashi Zuwa Dubu 100 Ko 200 – NLC
- Gwamnatin Kano Ta Ayyana Labara A Matsayin Hutu Saboda Bikin Maulidi
Gabriel Jesus ne ya fara jefa kwallo a ragar Lens kafin Thommarson da Wahi su jefa wa Lens kwallaye biyu.
A wasan ne kuma hazikin dan kwallon Arsenal Bukayo Saka ya samu raunin da har ya sa dole aka fitar da shi daga filin wasan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp