• English
  • Business News
Tuesday, October 28, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ashirye Muke Mu Amsa Duk Kura-kuran Da ‘Yan Jarida Suka Gano A Gwamnatinmu – Tinubu 

by Sulaiman
2 years ago
Tinubu

Shugaba Bola Tinubu ya ƙara jaddada cewa gwamnatinsa a ko yaushe za ta mutunta ‘yancin kafafen yaɗa labarai da ‘yan jarida, kuma za ta yi maraba hannu biyu da ra’ayoyin masu nuni da yin gyara – suka ko yabon gwamnatinsa.

Cikin sanarwar da Kakakin Yaɗa Labaran Shugaban Ƙasa, Ajuri Ngelale ya fitar, ya ce Tinubu ya yi wannan bayani ne ranar Litinin, lokacin da ya gana da mambobin Ƙungiyar Mawallafa Jaridu ta Nijeriya (NPAN).

  • Malamai A Kano Sun Gabatar Da Addu’o’i Kan Allah Ya Tabbatarwa Gawuna Nasararsa A Kotun Ƙoli
  • Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Da Zaben Tambuwal Da Wamakko A Matsayin Sanatoci

Shugaba Tinubu ya tabbatar masu da cewa zai zauna a tsanake ya duba buƙatar da suka bijiro masa da ita, wato ta neman a sassauta tsarin hada-hadar takardar buga jarida, wanda ke ci wa gidajen jaridu tuwo a ƙwarya ta hanyar tsadar takardun a cikin gida.

Da ya koma kan wahalhalun da matafiya ke fuskanta a yanzu lokacin tafiya hutun Kirsimeti da sabuwar shekara, Shugaba Tinubu ya ce gwamnatin tarayya za ta ɗauki matakan sauƙaƙa tsadar zirga-zirga da sufurin jiragen sama, na ƙasa da kuma kan titinan motoci.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris ne ya jagoranci tawagar masu gidajen jaridun a wannan ziyarar da suka kai wa Shugaba Tinubu.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Kashe Masu Yi Wa ISWAP 4 Safarar Makamai A Borno

APC Ta Yi Barazanar Dakatar Duk Kwamishinan Da Bai Sanya Irin Hular Tinubu Ba

Shugaban ya ci gaba da cewa ana nan ana ɗaukar matakan da za a rage farashin gas.

“Na damu sosai dangane da abin da ke faruwa a cikin ƙasar nan. Ina gode maku kan goyon bayan da ku ke bayarwa da ra’ayoyi da sukar da ake yi wa gwamnatin mu. Ba domin goyon bayan wasu daga cikin ku ba, ba zan zama shugaban ƙasa ba, har ga ni a yanzu tare da ku a matsayin shugaba.

“Kun jajirce kan aikin ku cikin rintsi da tsanani. Don haka mu kuma za mu ci gaba da mutunta ra’ayoyin ku, ko da kuwa ba mu yarda da abin da ku ka faɗa kan mu ba.

“Abu ɗaya da zan faɗa maku shi ne, ina karanta kowace jarida, ina kuma karanta ra’ayoyin da ake rubutawa, har ma da shafukan manazarta da marubuta ra’ayoyi daban-daban,” inji Tinubu.

A jawabin sa, Ministan Yaɗa da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya jaddada kyakkyawar aniyar Gwamnatin Tarayya ta shata wa kafafen yaɗa labarai kyakkyawar shimfiɗa a ƙasar nan.

“Dimokraɗiyyar mu ta ginu ne a kan tsari da tafarkin ƙa’ida da tabbatar da komai bisa kyakkyawan tsarin doka da kuma ‘yancin yaɗa labarai da bayanai.

“Rawar da kafafen yaɗa labarai musamman jaridu ke bayarwa ta na da tasiri da muhimmanci a wannan turbar dimokraɗiyya,” cewar Minista Idris.

Daga nan Idris ya jinjina wa jagororin NPAN saboda samar da ƙungiya mai ƙarfin tattauna batutuwan da suka shafi ƙasa da kuma bayar da damar sauraren muryoyin jama’a mabambanta ra’ayoyi da fahimta.

Shi kuma Shugaban NPAN, kuma shugaban kamfanin Media Trust, masu buga Daily Trust, Trust TV da Aminiya, Malam Kabiru Yusuf, ya fara da yi wa Shugaba Tinubu murnar nasarar zaɓe da kuma nasara a Kotun Ƙoli. Daga nan ya ci gaba da lissafo matsalolin da suka dabaibaye masana’antu da hada-hadar takardar buga jaridu.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno
Manyan Labarai

Sojoji Sun Kashe Masu Yi Wa ISWAP 4 Safarar Makamai A Borno

October 28, 2025
Tinubu
Manyan Labarai

APC Ta Yi Barazanar Dakatar Duk Kwamishinan Da Bai Sanya Irin Hular Tinubu Ba

October 27, 2025
Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Da Burgediya Janar Yake a Matsayin Sarkin Ƙabilar Sayawa
Manyan Labarai

Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Da Burgediya Janar Yake a Matsayin Sarkin Ƙabilar Sayawa

October 27, 2025
Next Post
Wani Mutum Ya Halaka Sakataren Kotu Har Lahira A Jihar Adamawa

Wani Mutum Ya Halaka Sakataren Kotu Har Lahira A Jihar Adamawa

LABARAI MASU NASABA

An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

Sojoji Sun Kashe Masu Yi Wa ISWAP 4 Safarar Makamai A Borno

October 28, 2025
Tinubu

APC Ta Yi Barazanar Dakatar Duk Kwamishinan Da Bai Sanya Irin Hular Tinubu Ba

October 27, 2025
An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka

An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka

October 27, 2025
Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani

Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani

October 27, 2025
Ribar Manyan Masana’antun Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.2 Cikin Dari A Watanni Tara Na Farkon Bana

Ribar Manyan Masana’antun Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.2 Cikin Dari A Watanni Tara Na Farkon Bana

October 27, 2025
Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Da Burgediya Janar Yake a Matsayin Sarkin Ƙabilar Sayawa

Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Da Burgediya Janar Yake a Matsayin Sarkin Ƙabilar Sayawa

October 27, 2025
Yawan Jigilar Kayayyakin Dake Bukatar Kankara a Kasar Sin Ya Zarce Tan Miliyan 117 a Watannin Yuni Da Yuli Da Agusta

Yawan Jigilar Kayayyakin Dake Bukatar Kankara a Kasar Sin Ya Zarce Tan Miliyan 117 a Watannin Yuni Da Yuli Da Agusta

October 27, 2025
Sin Za Ta Yi Tsayin Daka Wajen Kare Tsarin Cinikayya Tsakanin Mabanbantan Sassa

Sin Za Ta Yi Tsayin Daka Wajen Kare Tsarin Cinikayya Tsakanin Mabanbantan Sassa

October 27, 2025
Xi Ya Halarci Nune-Nune A Babban Gidan Adana Kayan Tarihi Na Karni

Xi Ya Halarci Nune-Nune A Babban Gidan Adana Kayan Tarihi Na Karni

October 27, 2025
Shugaba Tinubu Ya Gana Da Sabbin Hafsoshin Tsaro

Shugaba Tinubu Ya Gana Da Sabbin Hafsoshin Tsaro

October 27, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.