Hukumar kula da asibitin koyarwa ta tarayya a Gombe (FTH), ta haramtawa ma’aikatanta shiga ayyukan Kiripto ko duk wani nau’in abu makamancin haka a lokutan aiki.
A cewar hukumar kula da asibitin ta lura da yadda harkokin Kiripto ke ɗauke hankalin ma’aikata wajen kula da majinyata yadda ya kamata.
- Gwamnan Gombe Ya Jaddada Kudurin Tallafa Wa Matasa Ta Hanyar Fasahar Zamani
- Gwamnan Gombe Ya Kafa Doka Kan Hakar Ma’adanai Don Kare Muhalli
Cikin wata sanarwar cikin gida da hukumar asibitin ta fitar ta bayyana cewa ma’aikatan na da ‘yancin yin wasu ayyuka a lokacin da ba sa bakin aiki.
Da yake bayyana dalilin bayar da umarnin, mataimakin daraktan gudanarwa na Asibitin, Adamu Usman Tela, ya tabbatar da cewa sun ɗauki wannan mataki ne a matsayin rigakafi don gujewa samun koke-koken rashin kula da marasa lafiyar.
Sanarwar ta kara da cewa, tuni hukumar ta samar da kafar tura ƙorafi ta hanyar SERVICOM da ACTU, da jami’an da za su sanya ido da tabbatar da bin umarnin.
A kwanan nan dai ayyukan Kiripto sun zama ruwan dare a tsakanin matasan Nijeriya ciki har da masu karbar albashi.