Rundunar ‘yansandan jihar Ekiti ta nuna wani yaro mai kimanin shekara19 da ke zaune a Ado-Ekiti, bisa zargin da ake yi masana kwashe kudaden da ake bayarwa na gudummowa a cocin Osun, bayan ya sace naira 600,000.
Mai magana da yawun rundunar ‘yansanda na jihar DSP Sunday Abutu, ne ya bayyana haka ga manema labarai, wanda kuma ya ce, tun lokacin da ke bincike, wanda ake zargin ya tabbatar da laifinsa.
- Mauludi: Buhari Ya Bukaci ’Yan Siyasa Su Guje Wa Amfani Da Kalaman Batanci
- Samar Da Ingantattun Bayanan Kidaya Sirri Ne Na Kyakkyawan Ci Gaba – Ganduje
Ya ce, sun kuma kama wasu mutum 18 su kuma da ake zarginsu da laifin yin garkuwa da fashi da makami da kuma tsafi.
Abutu ya ci gaba da cewa, wadanda aka Kaman na daga cikin wadanda suka addabi wannan yanki da aikata miyagun laifuka.
Sannan ya kuma nuna kayan da aka kama wadannan mutanen da su, wadanda ake zargin cewa na sata ne.
Abutu ya tabbatar da cewa, rundunar ‘yansandan za ta ci gaba da yaki da bata-gari a dukkan fadin jihar, har sai ta kawo karshensu.