Gwamnatin Jihar Zamfara ta tabbatar da kisan riƙaƙƙen ɗan bindiga, Kachalla Ɗanbokolo da ya addabi wasu yankunan jihar.
Mai Bai Wa Gwamnan Jihar Shawara Kan Harkokin Tsaro, Ahmad Manga ya bayyana kisan Ɗanbokolo a matsayin gagarumin nasara a yaƙi da matsalar tsaro.
- Xi Jinping Ya Jaddada Niyyar Gina Babbar Kasuwar Kasa Ta Bai Daya, Tare Da Raya Tattalin Arziki Na Teku Mai Inganci
- Sin Za Ta Gabatar Da Shagulgulan Al’adu Na Bikin Cika Shekaru 80 Da Samun Nasarar Yaki Da Zaluncin Japanawa
”Ɗanbokolo mutum ne da ya fi Bello Turji fitina, ya fi Turji aikata miyagun laifuka, illa kawai shi Turji sunansa da ya karaɗe kafofin yaɗa labarai”, inji Ahmad Manga.
”Mutanensa da aka kashe sun haura 100, saboda haka wannan gagarumar nasara ce a gare mu”, inji shi.
Kacalla Ɗanbokolo ya rasa ransa ne a wata arangama a ƙauyen Kurya, tsakanin Askarawan Zamadara na gwamnatin jihar Zamfara da mayaƙan ɗan bindigar.
Ana kallon mutuwar Ɗanbokolo – wanda ake ganin a matsayin ubangidan Bello Turji – a matsayin ci gaba a ɓangaren yaƙi da ‘yan bindiga.
Ɗanbokolo ya shafe shekaru masu yawa yana kai hare-hare yankunan jihar Zamfara tare da sace mutane domin neman kuɗin fansa.
Riƙaƙƙen ɗan bindigar ya gamu da ajalinsa ne tare da wasu ɗimbin mayaƙansa a lokacin da Askarawan Zamfara – da gwamnatin jihar Zamfara ta samar.
Mazauna yankin na kallonsa a matsayin mutum marar imani da tausayi da ya addabi yankunansu, ta hanyar kai hare-hare da kisan mutane.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp