• English
  • Business News
Wednesday, October 29, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Asusun CFRD Ya Samu Yabo A Kasar Habasha

by CMG Hausa
3 years ago
CFRD

Asusun raya karkara na kasar Sin ko CFRD a takaice, ya samu yabo da jinjina, bisa managartar ayyukansa a kasar Habasha, a gabar da aka yi bikin cikarsa shekaru 3 da bude ofishinsa a kasar Habasha.

Asusun CFRD ya fara gudanar da ayyuka daban daban a Habasha tun daga shekarar 2015, an kuma yi masa rajistar gudanar da ayyuka a matsayin asusun ba da tallafin jin kai na kasa da kasa a kasar a watan Yulin shekarar 2019, inda ya maida hankali ga zurfafa hadin gwiwar musaya tsakanin al’ummun Sin da na kasar Habasha.

  • Ya Kamata A Bar Sinawa Su Yanke Shawara Kan Al’amuran Kasar Sin

Da yake jawabi yayin bikin na jiya Litinin, babban daraktan kungiyoyi masu zaman kansu na kasar Habasha Jima Dilbo, ya ce asusun CFRD ya shafe shekaru 7 yana gudanar da ayyuka daban daban a Habasha, ciki har da ciyar da daliban makarantu, da raba kayan karatu, da kayan abinci, da ruwan sha da ayyukan tsaftar muhalli, da ayyukan bunkasa tattalin arzikin mata, ayyukan da suka amfani sama da ’yan kasar Habashan 250,000.

Mr. Dilbo ya kara da cewa, dukkanin ayyukan CFRD, sun yi daidai da muhimman ayyukan da gwamnati da al’ummun Habasha ke bukata, wadanda ke da matukar tasiri ga ci gaban kasar.

Jami’in ya kuma yi kira ga asusun na CFRD, da ya jagoranci kungiyoyi masu zaman kansu dake Habasha, wajen kulla alaka da sauran kungiyoyi da hukumomi na kasa da kasa, kamar shirin samar da ci gaba na kasa da kasa, da na hadin gwiwar bunkasa kasashe masu tasowa, da shirin ziri daya da hanya daya. (Saminu Alhassan)

LABARAI MASU NASABA

Sabon Ingantaccen Hadin Gwiwar “Sin-ASEAN 3.0″ Ya Kafa Sabon Misali Na Hadin Kan Yanki

An Yi Taron Tataunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Moscow, Manama, Da Budapest

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sabon Ingantaccen Hadin Gwiwar “Sin-ASEAN 3.0″ Ya Kafa Sabon Misali Na Hadin Kan Yanki
Daga Birnin Sin

Sabon Ingantaccen Hadin Gwiwar “Sin-ASEAN 3.0″ Ya Kafa Sabon Misali Na Hadin Kan Yanki

October 29, 2025
An Yi Taron Tataunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Moscow, Manama, Da Budapest
Daga Birnin Sin

An Yi Taron Tataunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Moscow, Manama, Da Budapest

October 29, 2025
An Samu Ingantuwar Yanayin Iska Da Ruwa Cikin Watanni 9 Na Farkon Bana A Sin
Daga Birnin Sin

An Samu Ingantuwar Yanayin Iska Da Ruwa Cikin Watanni 9 Na Farkon Bana A Sin

October 29, 2025
Next Post
Ambaliyar Ruwa: FRSC Ta Shawarci Matafiya Da Su Kauracewa Hanyar Lokoja Zuwa Abuja

Akwai Yiwuwar Afkuwar Wata Sabuwar Ambaliyar Ruwa A Wasu Jihohi - NiMet

LABARAI MASU NASABA

Asuu

Gwamnatin Tarayya Ta Saki Naira Biliyan 2.3 Ga ASUU

October 29, 2025
Sabon Ingantaccen Hadin Gwiwar “Sin-ASEAN 3.0″ Ya Kafa Sabon Misali Na Hadin Kan Yanki

Sabon Ingantaccen Hadin Gwiwar “Sin-ASEAN 3.0″ Ya Kafa Sabon Misali Na Hadin Kan Yanki

October 29, 2025
Sulhu Da ’Yan Bindiga Ba Tare Da Sun Ajiye Makamai Ba Tamkar Miƙa Wuya Ne – Gwamna Lawal ga Hukumomin Tsaro

Sulhu Da ’Yan Bindiga Ba Tare Da Sun Ajiye Makamai Ba Tamkar Miƙa Wuya Ne – Gwamna Lawal ga Hukumomin Tsaro

October 29, 2025
An Yi Taron Tataunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Moscow, Manama, Da Budapest

An Yi Taron Tataunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Moscow, Manama, Da Budapest

October 29, 2025
majalisar kasa

Majalisar Wakilai Ta Amince Da Bukatar Amso Bashin Dala Biliyan 2.34 A Kasuwar Jari Ta Duniya

October 29, 2025
An Samu Ingantuwar Yanayin Iska Da Ruwa Cikin Watanni 9 Na Farkon Bana A Sin

An Samu Ingantuwar Yanayin Iska Da Ruwa Cikin Watanni 9 Na Farkon Bana A Sin

October 29, 2025
Kotu Ta Umarci Ƙwace Dala 49,700 Daga Tsohon Jami’in INEC

Kotu Ta Umarci Ƙwace Dala 49,700 Daga Tsohon Jami’in INEC

October 29, 2025
Yadda Kasar Sin Ke Kara Kyautata Tsarin Kare Muradun Al’umma A Bangaren Shari’a

Yadda Kasar Sin Ke Kara Kyautata Tsarin Kare Muradun Al’umma A Bangaren Shari’a

October 29, 2025
COAS Shaibu Ya Sha Alwashin Murƙushe ‘Yan Ta’addar Lakurawa 

COAS Shaibu Ya Sha Alwashin Murƙushe ‘Yan Ta’addar Lakurawa 

October 29, 2025
Binciken ‘Yan Sanda Kan Wanda Ake Zargi Da Tawayen “‘Yancin Kan Taiwan” Mataki Ne Na Adalci Don Kare Hadin Kan Kasa

Binciken ‘Yan Sanda Kan Wanda Ake Zargi Da Tawayen “‘Yancin Kan Taiwan” Mataki Ne Na Adalci Don Kare Hadin Kan Kasa

October 29, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.