A yau Litinin asusun ba da lamuni na duniya (IMF) ya kaddamar da aiki a cibiyarsa ta shiyyar Asiya da Pasifik dake birnin Shanghai na kasar Sin, karkashin babban masanin tattalin arziki na asusun Johannes Wiegand, a matsayin darakta.
A matsayin daya daga cibiyoyin IMF a fadin duniya, ana sa ran cibiyar ta Shanghai za ta inganta ayyukan IMF a yankin Asiya da tekun Pasifik.
Yayin bikin bude cibiyar, gwamnan babban bankin Sin Pan Gonsheng, ya ce kaddamar da cibiyar ta nuna matsaya mai karfi ta Sin da IMF ta goyon bayan hadin gwiwar moriyar juna. (Mai fassara: FMM)
ADVERTISEMENT














