Wakilin asusun ba da lamuni na duniya IMF a kasar Ghana Leandro Medina, ya jinjinawa gudummawar da kasar Sin ta bayar, a fannin goyon bayan matakan kasar Ghana na warware basussukan ta.
Leandro Medina, ya bayyana hakan ne yayin ganawar baya bayan nan da ya yi da jakadan kasar Sin a kasar ta Ghana Lu Kun. Jami’in ya kara da cewa, kasar Sin ta taka rawar gani a matsayinta na bangare guda, dake jagorantar kwamitin lura da basussukan kasar ta Ghana, kuma asusun IMF a shirye yake da ya ci gaba da zurfafa hadin gwiwa da kasar Sin, tare da ba da gudummawa ga warware basussukan da ake bin kasar ta Ghana.
Shi kuwa a nasa bangare, Lu Kun cewa ya yi, Sin za ta ci gaba da yin hadin gwiwa da dukkanin sassa, tare da aiwatar da matakai na hakika, domin tallafawa Ghana wajen aiwatar da manufofi masu dorewa na daidaita basussukanta. Kaza lika Lu ya ce Sin a shirye take ta zurfafa hadin gwiwa da IMF, wajen ingiza kyawawan manufofin jagorancin kasa da kasa bisa adalci da daidaito.
A baya bayan nan asusun IMF, ya amince da baiwa kasar Ghana lamunin dalar Amurka biliyan 3, ya kuma mika wa kasar dala miliyan 600 a karon farko, domin tallafa mata shawo kan kalubalen tattalin arziki da take fuskanta a halin yanzu. (Saminu Alhassan)