Shugaban ƙungiyar malaman jami’o’i na ƙasa (ASUU), Farfesa Emmanuel Osodeke, ya yi watsi da sabon naɗin da gwamnatin tarayya ta yi na shugabannin jami’o’in a kwanakin nan.
Osodeke wanda ya bayyana sabon jerin sunayen a matsayin mafi muni fiye da na baya, ya koka kan yadda ‘yan siyasa ke da yawa ciki, yana mai nuni da cewa naɗa su a shugabanin gudanarwar na da illa ga ci gaban jami’o’in Najeriya.
- Dakatar Da Albashin Sabbin Ma’aikatan Kano: Nakasassu Sun Shiga Tsaka-mai-wuya —Zango
- Ministan Yaɗa Labarai Ya Kafa Kwamitin Kare Haƙƙoƙin Naƙasassu
Ya ƙara da cewa, tsarin da ake bi a halin yanzu yana gurgunta harkokin gudanarwa da ci gaban manyan makarantu.
A baya dai ƙungiyar ASUU, ta yi fatali da sahihancin matakin da gwamnatin tarayya ta ɗauka na kafa sabbin majalissar gudanarwa yayin da wa’adin majalisun da aka rusa tun watanni 10 da ya gabata bai kare ba.
Matakin a cewar ASUU, ya saɓawa dokar jami’o’i, wadda ta ƙayyade tsawon wa’adin shugabancin nasu, tare da tabbatar da cewa irin waɗannan naɗe-naɗen siyasa ba su yi daidai da ƙa’idojin ilimi da gudanarwa da ake buƙata domin samar da ci gaba na haƙiƙa a jami’o’in ƙasar nan ba.