Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Nijeriya (ASUU) ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki 14 don biyan buƙatunta da ba a warware ba.
Wannan matakin ya biyo bayan taron majalisar koli na ƙungiyar (NEC), da aka gudanar a ranar Lahadi a Jami’ar Abuja.
- Kasashen Sin Da Afrika Za Su Hada Kai A Bangaren Intanet
- Kotu Ta Dakatar Da PENGASSAN, NNPCL Kan Katse Wa Matatar Ɗangote Ɗanyen Mai Da Iskar Gas
Shugaban ASUU, Farfesa Chris Piwuna, ya bayyana a wata sanarwa a ranar Litinin cewa idan gwamnati ta gaza ɗaukar mataki cikin kwanaki 14, za su fara da yajin aikin gargaɗi na makonni biyu, sannan daga baya su tsunduma yajin aikin da babu ranar dawowa.
Ya zargi gwamnati da yin watsi da jami’o’i da kuma ƙin sauraron buƙatun ƙungiyar.
Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta kafa wani kwamitin da Abel Enitan, Babban Sakataren ma’aikatar, ke jagoranta domin nazarin shawarwarin ASUU.
Buƙatun da ASUU ke nema sun haɗa da: sake duba yarjejeniyar 2009 tsakaninsu da gwamnati, samar da ƙarin kuɗaɗen bunƙasa jami’o’i, biyan bashin albashin da suke bi, da samar da ingantaccen tsarin kuɗi mai ɗorewa ga jami’o’i.