Ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa (ASUU) ta raba kayan abinci ga ‘yan gudun hijira 320 da ke jihar Katsina a ranar Lahadi.
Dakta Lawalli Alkali, shi ne ya wakilci shugaban ƙungiyar na ƙasa, Farfesa Victor Emmanuel a yayin rabon kayan rage raɗaɗin.
- Za A Kammala Aikin Bututun Iskar Gas Na AKK A Disambar 2024 – NNPC
- An Yi Garkuwa Da Iyayen Dan Wasan Liverpool Luis Diaz A Colombia
Ya ce, wannan ba shi ne irinsa na farko da ƙungiyar ta ke yin irin wannan tallafin ba, inda ya ce, irin wannan na ɗaukan lokaci kafin su yi, amma ba shi ne na farko ba.
Ya ce, kayan abincin sun haɗa da shinkafa, mangyaɗa, taliyar leda, taliyar yara, magin ɗanɗano da dai sauransu.
Ƙungiyar ta ce, ta fahimci ‘yan gudun hijira a matsayin mutanen da ke fama da matsala da ke tsananin buƙatar tallafi da agaji, don haka ne ƙungiyar ta ayyanasu cikin al’ummar da ke neman tallafi.
Alkali ya roƙi shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya yi dukkanin mai yiyuwa domin shawo kan matsalolin tsaro da suke faɗin ƙasar nan domin bai wa ‘yan gudun hijira damar komawa gidajensu na asali.
A cewarsa, ASUU na bibiyar lamura a jihar Katsina don haka ne suka jinjina wa ƙoƙarin gwamna Dikko Radda na matakan da ya ke ɗauka kan matsalar tsaro.
Wasu ‘yan gudun hijiran waɗanda mafi yawansu mata ne sun yaba wa ƙungiyar ASUU bisa tallafin, inda suka roƙi gwamnatin jihar da ɗaiɗaikun mutane su ma da su taimaka musu.