Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), reshen Jami’ar Jihar Taraba (TSU), ta ayyana yajin aikin sai baba-ta-gani saboda gazawar gwamnatin jihar wajen aiwatar da yarjejeniyar albashi ta shekarar 2025 tsakanin Gwamnatin Tarayya da ASUU.
Ƙungiyar ta sanar da fara cikakken yajin aikin nan take, tana mai cewa matakin ya kuma kara dagulewa ne biyo bayan rashin biyan malaman alawus tun daga watan Janairun 2026.
Jaridar LEADERSHIP ta ruwaito cewa ASUU ta ɗauki wannan mataki ne bayan shafe watanni tana tattaunawa da gwamnatin jihar kan buƙatunta.
An bayyana ayyana yajin aikin ne a cikin wata sanarwa da Shugaban ASUU na Jami’ar Jihar Taraba, Dr Joshua Garba Mbave, ya sanya wa hannu a ranar Litinin.
Ya ce yajin aikin ya zama dole, bayan gwamnatin jihar ta gaza aiwatar da tsarin biyan albashin da aka amince da shi, duk da kammala aikin tantance bayanai da kuma ƙarewar ƙarin lokacin da hukumomin suka nema domin cika yarjejeniyar.













