Dan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya kayar da abokin fafatawarsa na APC, Bola Ahmed Tinubu a zaben da aka gudanar na shugaban kasa a ranar Asabar a Jihar Bauchi.
Atiku ya samu nasara a kananan hukumomi 18 yayin da Tinubu ya samu nasara a kananan hukumomi biyu na Toro da Itas/Gadau.
- INEC Ta Ayyana Shekarau A Matsayin Wanda Ya Lashe Zaben Sanatan Kano Ta Tsakiya
- Kwankwaso Ya Lashe Kano, Ya Bai Wa Tinubu Da Atiku Gagarumar Tazara
Da ya ke sanar da sakamakon zaben, baturen tattara sakamakon zaben a Jihar Bauchi, Farfesa Abdulkadir Sabo Muhammad, mukaddashin shugaban Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse a Jihar Jigawa, ya ce Atiku ya samu kuri’u 426,607.
Tinubu ya samu kuri’u 316,694 da ya zo na biyu, inda kuma dan takarar NNPP ya samu kuri’u 72,103 sai LP, Peter Obi 27,373.
Farfesa Sabo ya sanar da cewa adadin masu zabe a jihar Bauchi 2,749,268; wadanda aka tantance 899,769, inda aka samu kuri’u masu kyau 853,516 sannan an soke 29,030. Baya ga hakan adadin kuri’u 882,546 ne aka kada ya zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar Asabar din da ta gabata.