Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi, ya sanya kafa ya shure hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa (PEPC), ta yanke da ta tabbatar wa Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC nasararsa.
Kotun dai a ranar Labara ta ce Tinubu ya lashe zaben sa na ranar 25 ga watan Fabrairu.
- Yadda Tinubu Ya Yi Nasara Kan Abokan Hamayyarsa Atiku Da Obi
- Ka Daina Gararamba A Titi Ka Tafi Kotu —Martanin APC Ga Atiku
Obi a wani taron manema labarai da ya gudanar a ranar Alhamis kasa da ‘yan awanni bayan da takwaransa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya sanar da irin wannan matsayar.
LEADERSHIP ta labarto cewa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a taron manema labarai a ranar Alhamis da jam’iyyarsa ta PDP sun ki amincewa da amsar hukuncin da PEPC ta yanke da ke tabbatar da nasarar Tinubu a babban zaben 2023.
Idan za ku tuna a ranar Labara kotun ta yanke hukuncin kan kararrakin da PDP, LP da Allied Peoples Movement (APM) da ‘yan takararsu suka shigar a gabanta suna kalubalantar nasarar Tinubu da APC.
Obi, a taron manema labarai a Abuja ya ce tunin ya umarci Lauyoyinsa da su daukaka kara kan hukuncin PEPC zuwa kotun Koli kamar yadda kundun tsarin mulkin kasa na 1999 (da aka yi wa kwaskwarima) suka tanadar.
Shi ma Atiku Abubakar ta tabbatar da cewa tunin ya ce wa Lauyoyinsa su gaggauta su kuma hanzarta tafiya kotun Koli domin nuna rashin gamsuwa da hukuncin na kotun sauraron kararrakin zaben.
Atiku da Obi sun ce hukuncin cike yake da kurakurai don haka ba su aminta da shi ba.