• Leadership Hausa
Monday, May 29, 2023
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ka Daina Gararamba A Titi Ka Tafi Kotu —Martanin APC Ga Atiku

by Sadiq
3 months ago
in Manyan Labarai
0
An Kai Wa Magoya Bayan Atiku Hari A Gombe
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Jam’iyyar APC ta shawarci dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar da ya sa lauyoyinsa su daukaka kara a gaban kotu maimakon gudanar da zanga-zanga a titunan kasar nan.

Mista Bayo Onanuga, Daraktan yada labarai na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC ne, ya bayar da shawarar a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Abuja.

  • Jam’iyyar NNPP Ta Bukaci Jami’an Tsaro Su Tabbatar An Yi Sahihin Zabe A Kano
  • Kotun Koli Ta Tabbatar Lawal Dare A Matsayin Dan Takarar Gwamnan PDP A Zamfara 

Bayanin hakan dai shi ne martanin jam’iyyar APC ta fitar kan zanga-zangar da ‘yan jam’iyyar PDP suka shirya a karkashin Atiku na nuna adawa da sakamakon zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya na ranar 25 ga watan Fabrairu.

Onanuga ya kuma shawarci Atiku da ya mutunta shekarunsa da kuma babban ofishin mataimakin shugaban kasar Nijeriya da ya taba yi.

“Lokacin da Atiku Abubakar da ya sha kaye ya shaida wa duniya a makon da ya gabata cewa zai nemi hakkinsa a kotu kan sakamakon zabe, don haka ko kadan ba mu san cewa zai tafi kotu ba.

Labarai Masu Nasaba

Abubuwa 10 Da Zaku So Sani Cikin Jawabin Bankwana Da Buhari Ya Yi Wa ‘Yan Nijeriya

Ganduje Zai Mika Wa Abba Gida-Gida Ragamar Mulkin Kano, Don Halartar Rantsar Da Tunibu

“Bisa ga magabata na siyasa, ba abin mamaki ba ne, cewa Atiku, kwanaki bayan haka, ya jagoranci gungun masu zanga-zanga, a Abuja zuwa hedikwatar Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC).

“Abin da Alhaji Atiku da jama’arsa suka nuna a yau wani sabon salo ne daga wanda ya sha kaye a zabe.

“A yayin da Atiku ya shirya wasan kwaikwayo na banza, mun kasa ganin yadda tattakin da jama’a da dama suka yi zuwa INEC zai samar da duk wata nasarar da ya samu a gare shi da ‘yan jam’iyyarsa ta PDP,” in ji Onanuga.

Atiku dai da jiga-jigan jam’iyyar PDP sun yi zanga-zangar nuna adawa da sakamakon zaben da INEC ta ayyana Tinubu a matsayin zababben shugaban kasar Nijeriya.

Tags: APCAtikuINECKotuPDPZanga-zangaZwben Shugaban Kasa
ShareTweetSendShare
Previous Post

Ba Za Mu Bari NNPP Ta Yi Magudin Zabe A Kano Ba —Gwamnatin Kano

Next Post

Tinubu Ya Yi Allah Wadai Da Harin Zamfara Da Kano

Related

Abubuwa 10 Da Zaku So Sani Cikin Jawabin Bankwana Da Buhari Ya Yi Wa ‘Yan Nijeriya
Manyan Labarai

Abubuwa 10 Da Zaku So Sani Cikin Jawabin Bankwana Da Buhari Ya Yi Wa ‘Yan Nijeriya

1 day ago
Ganduje Zai Mika Wa Abba Gida-Gida Ragamar Mulkin Kano, Don Halartar Rantsar Da Tunibu
Manyan Labarai

Ganduje Zai Mika Wa Abba Gida-Gida Ragamar Mulkin Kano, Don Halartar Rantsar Da Tunibu

1 day ago
Na Gyara Nijeriya Fiye Da Yadda Na Same Ta A 2015 – Buhari
Manyan Labarai

Na Gyara Nijeriya Fiye Da Yadda Na Same Ta A 2015 – Buhari

1 day ago
An Ci Gaba Da Jefa Kuri’a A Zaben Turkiyya Zagaye Na Biyu A Yau Lahadi
Manyan Labarai

An Ci Gaba Da Jefa Kuri’a A Zaben Turkiyya Zagaye Na Biyu A Yau Lahadi

1 day ago
Ba Ma Kokarin Musuluntar Da Nijeriya –Shettima
Manyan Labarai

Ba Ma Kokarin Musuluntar Da Nijeriya –Shettima

2 days ago
Kwankwaso Ba Zai Sauya Jam’iyya Ba -NNPP
Manyan Labarai

Kwankwaso Ba Zai Sauya Jam’iyya Ba -NNPP

2 days ago
Next Post
Tinubu Ya Yi Allah Wadai Da Harin Zamfara Da Kano

Tinubu Ya Yi Allah Wadai Da Harin Zamfara Da Kano

LABARAI MASU NASABA

Da Dumi-dumi: An Rantsar Da Tinubu A Matsayin Shugaban Nijeriya Na 16

Da Dumi-dumi: An Rantsar Da Tinubu A Matsayin Shugaban Nijeriya Na 16

May 29, 2023
A Dan Lokacin Da Ya Rage Kafin Mika Mulki: Buhari Ya Sauya Sunayen Filayen Jiragen Sama 15

A Dan Lokacin Da Ya Rage Kafin Mika Mulki: Buhari Ya Sauya Sunayen Filayen Jiragen Sama 15

May 29, 2023
Ana Bin Jihar Kano Bashin Sama Da Naira Biliyan 240, Inji Abba Gida-gida 

Ana Bin Jihar Kano Bashin Sama Da Naira Biliyan 240, Inji Abba Gida-gida 

May 29, 2023
Bankwana Da Gwamnatin Buhari: Hukumar Tsaron Cikin Gida Ta Kara Wa Jami’ai 17,331 Matsayi

Bankwana Da Gwamnatin Buhari: Hukumar Tsaron Cikin Gida Ta Kara Wa Jami’ai 17,331 Matsayi

May 29, 2023
Gwamnati Ta Samar Da Tan 89,512 Na Irin Noma A Bana – Minista

Gwamnati Ta Samar Da Tan 89,512 Na Irin Noma A Bana – Minista

May 29, 2023
Kwana Guda Ya Sauka, El-Rufai Ya Haramta Kungiyar Kudancin Kaduna

Kwana Guda Ya Sauka, El-Rufai Ya Haramta Kungiyar Kudancin Kaduna

May 29, 2023
Buhari Ya Nada Sha’aban Mukamin Babban Sakataren Hukumar Kula Da Almajirai Ta Nijeriya

Buhari Ya Nada Sha’aban Mukamin Babban Sakataren Hukumar Kula Da Almajirai Ta Nijeriya

May 28, 2023
An Wallafa Littafin Dake Kunshe Da Mukalolin Shugaba Xi Kan Dogaro Da Kai A Fannin Kimiyya Da Fasaha

An Wallafa Littafin Dake Kunshe Da Mukalolin Shugaba Xi Kan Dogaro Da Kai A Fannin Kimiyya Da Fasaha

May 28, 2023
Ganduje Yayi Jawabin Bankwana Tare Da Shirin Mika Mulki A Yau Lahadi

Ganduje Yayi Jawabin Bankwana Tare Da Shirin Mika Mulki A Yau Lahadi

May 28, 2023
Jihar Kano Ta Ayyana Masu Kwacen Waya A Matsayin ‘Yan Fashi Da Makami

Jihar Kano Ta Ayyana Masu Kwacen Waya A Matsayin ‘Yan Fashi Da Makami

May 28, 2023
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.