Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya yi imanin hadewar jam’iyyun adawar Nijeriya zai taimaka wajen samar da kyakyawar alaka wajen yakar jam’iyyar APC mai mulki.
Atiku wanda shi ne dan takarar jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasa na 2023, ya bayyana hakan ne a Abuja a ranar Talata lokacin da ya karbi bakuncin kwamitin zartarwa na kungiyar masu ba da shawara ta kasa (IPAC).
- BUK Ta Dakatar Da Jarabawa Sakamakon Yajin Aikin NLC Da TUC
- Babu Ranar Daina Amfani Da Tsofaffin Takardun Naira – CBN
“A yau, a lokacin wani taro da kwamitin zartarwa na kasa na kungiyar masu ba da shawara ta jam’iyyu (IPAC), na jaddada muhimmancin kare dimokuradiyyarmu.
“Na damu kan abubuwan da APC ta yi, inda ta mayar da Nijeriya mulkin kama-karya na jam’iyya daya. Na roki kungiyar IPAC karkashin jagorancin Yabagi Sani da ta hada jam’iyyun adawa don samar da wata kafa mai karfi a kan wannan barazana.
“Na soki INEC da gudanar da zabe mara inganci, ciki har da sabanin adadin masu zabe. Na yi kira ga Majalisar Dokoki ta kasa da ta ba da fifiko ga sauye-sauyen tsarin mulkin kasa da na zabe, musamman gyara game da fitar da sakamako ta hanyar nau’ra, don tabbatar da zabe na gaskiya da kare dimokuradiyyarmu.
‘Na yi imanin dimokuradiyya, duk da kurakuran da aka samu a lokacin zabe, ita ce mafi kyawun tsarin gwamnati, kuma na himmatu wajen hada kai da sauran jama’a wajen samar da tsaro a Nijeriya.”
Shugaban kungiyar na kasa, Yabagi Sani ne ya jagoranci tawagar IPAC wajen kai wa Atiku ziyara.