Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya karbi baƙuncin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi a gidansa da ke garin Yola a Jihar Adamawa.
Taron wanda aka wallafa faifan bidiyon a shafin Atiku na X (Twitter) a yau Asabar, ya nuna shugabannin biyu suna cin abinci tare inda Atiku ya rubuta sakon cewa, “Karin kumallo da abokina Peter Obi”.
- Dalilai 15 Na Muhimmancin Tsara Yadda Malami Zai Koyar Da Darussa A Aji (1)
- Filin Jiragen Sama Na Legas Da Abuja Sun Samu Cikakken Izinin Zirga-zirga Daga NCAA
Bidiyon ya nuna Atiku da Obi suna zaune a teburin cin abinci tare da wasu jiga-jigan ƙasar nan, suna tattaunawa wanda ke nuna wata muhimmiyar mu’amala tsakanin jiga-jigan siyasar biyu.
Ganawar tasu ta baya dai ta faru ne a watan Mayu, lokacin da Obi ya ziyarci Atiku, a gidansa da ke Abuja, inda ya gana da wasu jiga-jigan jam’iyyar adawa ta PDP da suka haɗa da tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido da tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki.
Mai magana da yawun ƙungiyar yakin neman zaben shugaban ƙasa na Peter Obi, Yunusa Tanko, a baya ya bayyana cewa tattaunawar da aka yi a watan Mayu, ta mayar da hankali ne kan tsara hanyar ceto Nijeriya daga ƙangin da ta ke ciki.
Duk da cewa ba a bayyana cikakken bayanin taron na baya-bayan nan ba, amma ana cece-kuce game da yiwuwar haɗin gwuiwa ko daidaita tsakanin manyan ‘yan adawar don tunkarar zaɓen 2027.