Mataimakin firaministan kasar Sin Liu Guozhong, ya ce Sin ta cimma nasarar takaita bazuwar cutar AIDS ko Sida zuwa mataki mafi kankanta, amma ya yi gargadi game da tarin kalubalolin dake tattare da ayyukan kandagarki da na shawo kan cutar.
Liu ya yi tsokacin ne yayin wani rangadin gani da ido da ya gudanar, a cibiyar kandagarki da shawo kan cututtuka ta kasar Sin ko “China CDC”, gabanin ranar cutar mai karya garkuwar jiki ta duniya, wadda za a yi bikinta a karo na 37, a gobe Lahadi 1 ga watan Disamba.
- Tawagar Mu’amalar Al’adu Ta Xinjiang Ta Kasar Sin Ta Kai Ziyara Turkiye Da Saudiyya Da Qatar
- “Nijeriya Na Asarar Dala Biliyan 492 Duk Shekara Kan Noƙe Haraji”
Mataimakin firaministan na Sin, ya ce yaki da cutar AIDS aiki ne mai muhimmanci a fannin gina tsarin kula da lafiya mai inganci na Sin. Kuma bisa jajircewar dukkanin sassan al’ummun Sin, kasar ta yi nasarar shawo kan bazuwarta zuwa mataki mafi kankanta.
To sai dai kuma, dalilan dake haddasa bazuwar cutar na da sarkakiya, sun kuma sha bamban, don haka kandagarkinta, da shawo kan cutar ke ci gaba da zama babban kalubale. Don haka ya yi kira da a karfafa sanya ido, da samar da tsarin gargadi na gaggawa, da aiki tukuru wajen tantancewa, da yin gwaje-gwaje, da aiwatar da cikakkun matakan da suka wajaba, na gaggauta gano masu dauke da cutar.
Liu ya kuma yi kira da a karfafa bincike, da samar da magunguna, da rigakafi, da sauran muhimman fasahohi na karfafa kimiyyar kandagarki, da maganin cutar ta AIDS ko Sida. (Saminu Alhassan)