Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya, Atiku Abubakar, ya sake kokawa kan yadda matsalar tsaro ke ci gaba da addabar ‘yan Nijeriya a sakamon ƙarin samun yawaitar kai hare-haren ‘yan ta’adda ba ƙaƙƙautawa.
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar, ya bayyana rashin jin ɗaɗinsa musamman kan yadda ake garkuwa da ƴan jarida da alƙalai da shugabannin ƙwadago da iyalansu a baya-bayan nan.
- Zargin Dokar Bai Wa Auren Jinsi Kariya: Gwamnatin Tarayya Ta Koka Kan Rahoton Wata Jarida
- Sojoji Da Mafarauta Sun Dakile Shirin ‘Yan Ta’adda Na Lalata Falwayar Wutar Lantarki A Yobe
Atiku ya bayyana damuwarsa kan lamarin a shafinsa na X, ya ce ” a wannan lokutan na tashin hankali, ƴan jaridarmu su ne ke haska wa al’umma, kuma ba sa yin ƙasa a guiwa wajen tabbatar da jagorori sun yi abin da ya kamata. Sai dai kuma abin takaici yanzu su ne ababan kai wa hare-hare.”
A bayanin nasa da ya wallafa, Atiku Abubakar ya kawo jerin lokutan da aka yi garkuwa da mutanen da yake nuna ɓacin ransa a kai hare-haren.