Mai magana da yawun ofishin dake lura da harkokin Taiwan a majalisar gudanarwar kasar Sin Zhu Fenglian, ta ce atisayen da dakarun rundunar sojojin ’yantar da al’umma na kasar Sin ko PLA shiyyar gabashin kasar ta kaddamar a kewayen tsibirin Taiwan, wani horo ne mai tsanani ga mahukuntan gwamnatin Lai Ching-te dake rajin “’yancin kan Taiwan”.
Zhu Fenglian ta bayyana hakan ne a Talatar nan, tana mai cewa atisayen wani gargadi ne ga sassan ’yan aware dake yunkurin gurgunta zaman lafiya a zirin Taiwan, kuma mataki ne da ya wajaba a dauka domin kare ikon mulkin kai da martabar yankunan kasar Sin.
Jami’ar ta kara da cewa, neman “’yancin Taiwan na nufin yaki, da ingiza al’ummarsa cikin mummunan hali”. A daya hannun, babban yankin kasar Sin na kan bakansa na tabbatar da nasarar warware batun Taiwan, da cimma manufar dinke dukkanin sassan kasar yadda ya kamata. Har ila yau, babban yankin na Sin ba zai taba amincewa da duk wasu ayyuka masu nasaba da neman ’yancin kan yankin Taiwan ba. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp