Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a yau Litinin cewa, atisayen da sojojin kasar Sin suka yi a mashigin tekun Taiwan wani muhimmin martani ne ga goyon bayan da kasashen waje ke nunawa kan yunkurin neman “’yancin kan Taiwan,” kuma babban gargadi ne ga ‘yan awaren Taiwan.
Kakakin ta ce, matakin soja da kasar Sin ta dauka ya wajaba, kuma yana bisa doka, ya kuma dace don kare ikon mallakar kasa, da tsaro da kuma cikakkun yankunanta.
Mao ta bayyana hakan ne a lokacin da take ba da amsa ga tambayoyi a taron manema labarai na yau, inda ta ce, rahotanni sun nuna cewa, sojojin kasar Sin sun gudanar da atisayen soji a mashigin tekun Taiwan a yau Litinin. Kuma an yi imanin cewa, atisayen na da nasaba da sauye-sauyen da aka yi a shafin yanar gizon ma’aikatar harkokin wajen Amurka a baya-bayan nan dangane da manufar Taiwan, da kuma ayyukan ‘yan aware masu neman ‘yancin kan Taiwan. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp