Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU), ta hannun hukumar bincike da ƙirkire-ƙirkire ta Afirka (AU-ASRIC), ta sake naɗa tsohon ministan sadarwa Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, a matsayin shugaban kwamitin tsarawa da bunkasa manufofin juyin+juya halin masana’antu ga kasashe 54 na Afirka karo na 4.
Pantami, wanda ya kasance babban mai bincike da mai yaɗa manufofin inganta masana’antu a duniya, shine ɗan Afirka na farko da ya fara samun lasisi da cibiyar tsaron bayanai ta Birtaniya.
- Shugaban Majalisa Ya Janye Ƙudirin Dokar Dauri Ga Wanda Ya Ki Rera Taken Nijeriya
- Kasar Sin Na Tir Da Harin Isra’ila Kan Makarantu A Gaza Tare Da Kira Da A Dakatar Da Bude Wuta
A baya ya taba rike mukamin Darakta Janar na Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Nijeriya (NITDA), inda ya fara kafa cibiyar fasahar kere-kere da mutum-mutumi (NCAIR) wacce ya kaddamar a lokacin da yake Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani.
Kazalika an zaɓi wata mai suna Anicia Nicola Peter, daga hukumar bincike da kimiya da fasaha ta ƙasar Namibiya, don ta kasance mataimakiyarsa, tare da wasu fitattun malamai da masu tsara manufofi, a majalisar irin su Farfesa Khaleed Ghedira daga Tunisia, da Farfesa Maha Grima daga Morocco, Farfesa Mongi Nouira, da Farfesa Munir Frija.
Da zarar dai ƙungiyar Tarayyar Afirkan ta amince da manufofin majalisar, ana sa ran dukkan ƙasashen za su fara aiwatar tsare-tsare da manufofin kwamitin don tafiya da nahiyar Afirka a fannin juyin-juya halin masana’antu da zai kai ga samun ci gaba mai mahimmanci a fannoni kamar da a turance ake Intelligence Artificial da Robotics da Blockchain da Tsaron Intanet.