• English
  • Business News
Saturday, October 25, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

AUREN DA NAKE BURI

by Sulaiman
3 years ago

LABARAI MASU NASABA

Neman Kudi Ne Ya Kawo Ni Masana’antar Kannywood Ba Fadakarwa Ba – Khadija Muhammad 

Me Ya Sa Jaruman Masana’antar Kannywood Ke Auren Sirri?

Fili na musamman domin matasa, wanda yake bawa ku masu karatu dama ku bayyana irin mace ko namijin da kuke son aura, tare da bayyana irin shagalin bikin da kuke son a yi muku, har ma da irin zaman auren da kuke son yi da masoyan naku. A yau ma ina tafe da wasu sakonnin naku kamar haka:

‘Zabina Shi Ne Namiji Dogo Fari Bugun Abuja’
Ni akan kaina ina son namiji dogo fari irin bugun Abuja kun dai gane, wanda kana kallonsa ka san daga cikin AC ya fito, kyakkyawa dan Beauty, mara jiki amma ba siriri ba, dan matsakaici, me dan kauri kadan, wanda kallonsa zai kasance kamar kallon soyayya, me kwantaccen gashin fuska wato saje da kuma gemu kwantacce kadan ba me yawa ba, wanda bakinsa yake dai-dai misali dan tsuwit gwanin birgewa, sannan dan gayu me saka kananan kaya dan ba na son manyan kaya ko zai saka ya zamo iya juma’a ce kawai ko kuma zuwa sallar idi ko wajen daurin aure, Allah ka ba ni. To fa irin auren da nake buri ai ni kowanne ne ma ya samu ina so muddin zan samu irin wanda na lissafo. Zaman auren da za mu yi, za mu yi rayuwar jin dadi ta birgewa, irin wadda ba za mu so mu rabu da juna ba, duk wani aiki da zan yi tare za mu yi, wajen aiki ma in da hali na bishi na zauna gefe in ya gama mu taho tare.
Daga Suhailat Idris Jihar Bauchi

‘Ina Son Namijin Da Ba Zan Ji Kunyar Shiga Da Shi Ko Ina Ba’
Auren da nake buri ina son na auri namiji Dan gayu wanda ba zan ji kunyar shiga da shi ko’ina ba, ban damu da fari ne shi ko baki, mai kiba ko akasin haka ba, kawai burina ya kasance Dan gayu, sannan ina son ya kasance mai kwalliya, amma fa babban mutum irin 60yrs din nan, wanda zai rinka riritani tamkar kwai akan cokali, wanda zai so ni kamar ya mai da ni cikinsa ya girmama iyayena tamkar su suka haife shi, ya aje ni a Lagos saboda mu rinka ziyartar tekuna, saboda ina son na ganni ni da shi a gabar ruwa na san wannan yanayin zai mana dadi sosai, amma fa ni ba zan zauna gida daya da matarsa ba ko yaransa ba.
Daga Hussy Saniey

‘Na Zabi Namiji Mara Girman Kai A Matsayin Miji’
Burina shi ne na auri namijin da ba shida girman kai, wanda in ya yi ba dai-dai ba matarsa ta yi masa gyara zai yarda da wannan gyaran da ta yi masa, Ina son namiji mai saukin kai ko da kuwa ba kyakkyawa bane, amma kuma bana son mummuna (Alllah na tuba), Ina son namiji mai tsafta, bana son kazami. Irin Auren da nake buri ayi min shi ne wanda za mu sha shagali irin na zamani bana son auren zamanin daya shude na fi son na dai-dai zamani na ba wai karya za a yi a bikin ba amma dai a bawa bikin hakkinsa yadda ya kamata. Irin zaman auren da nake son yi da mijina in Allah ya nufa, ina son mu yi zaman cikin soyayya kamar dai soyayya ta saurayi da budurwa bana son zaman da za ki ga namiji na hantarar mace bana son irinsa.
Daga Arfa Ibrahim Jihar Kebbi

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Neman Kudi Ne Ya Kawo Ni Masana’antar Kannywood Ba Fadakarwa Ba – Khadija Muhammad 
Nishadi

Neman Kudi Ne Ya Kawo Ni Masana’antar Kannywood Ba Fadakarwa Ba – Khadija Muhammad 

October 11, 2025
Me Ya Sa Jaruman Masana’antar Kannywood Ke Auren Sirri?
Nishadi

Me Ya Sa Jaruman Masana’antar Kannywood Ke Auren Sirri?

October 11, 2025
Kotu Ta Aike Da Ɗan TikTok Gidan Gyaran Hali Kan Bidiyon Batsa A Kano
Nishadi

Kotu Ta Aike Da Ɗan TikTok Gidan Gyaran Hali Kan Bidiyon Batsa A Kano

October 6, 2025
Next Post
Bukatar Koya Wa Yara Zama Lafiya Da Kowa

Bukatar Koya Wa Yara Zama Lafiya Da Kowa

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take

Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take

October 24, 2025
Ba Zan Kwatanta Matsayina Da Na Sarkin Bauchi Ba – Sabon Sarkin Duguri

Ba Zan Kwatanta Matsayina Da Na Sarkin Bauchi Ba – Sabon Sarkin Duguri

October 24, 2025
Gwamnatin Kaduna Ta Gano Ma’adanin Zinari Da Tagulla Da Za Su Haɓaka Tattalin Arziƙin Jihar

Gwamnatin Kaduna Ta Gano Ma’adanin Zinari Da Tagulla Da Za Su Haɓaka Tattalin Arziƙin Jihar

October 24, 2025
An Kebe Ranar 25 Ga Oktoba A Matsayin Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

An Kebe Ranar 25 Ga Oktoba A Matsayin Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

October 24, 2025

Gwamnatin Katsina Ta Ƙara Samar Da Dakarun Tsaro 200 Domin Maganace Ta’addanci

October 24, 2025
Sin Ta Saka Burikan Da Za Ta Cika A Shekaru 5 Masu Zuwa

Sin Ta Saka Burikan Da Za Ta Cika A Shekaru 5 Masu Zuwa

October 24, 2025
Jam’iyyar NNPP A Kaduna Ta Ƙaryata Batun Tsige Shugabanta

Jam’iyyar NNPP A Kaduna Ta Ƙaryata Batun Tsige Shugabanta

October 24, 2025
An Shirya Harba Kumbon Shenzhou-21 A Kwanan Nan

An Shirya Harba Kumbon Shenzhou-21 A Kwanan Nan

October 24, 2025
Shugaba Xi Ya Jagoranci Zaman Jin Ra’ayoyin Wadanda Ba ‘Yan JKS Ba Game Da Tsara Shirin Raya Kasa Karo Na 15 

Shugaba Xi Ya Jagoranci Zaman Jin Ra’ayoyin Wadanda Ba ‘Yan JKS Ba Game Da Tsara Shirin Raya Kasa Karo Na 15 

October 24, 2025
Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Wa Sarakuna Ba Zai Rage Musu Iko Ba A Shirinsa Na Ƙirƙirar Sabbin Masarautu

Gwamnan Bauchi Ya Naɗa Yayansa A Matsayin Sabon Sarkin Duguri

October 24, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.