Fili na musamman domin Matasa.wanda ke bawa kowa damar fadar irin Macen ko namijin da ake son aura, tare da irin shagalin bikin da ake son yi, gami da irin rayuwar auren da ake son yi. A yau ma muna tafe da kadan daga sakonnin da kuka turo kamar haka:
“Ina Son Namiji Mara Jiji Da Kai”
Ina son namiji mara jiji da kai, mai saukin kai, wanda komai ya yi na kuskure matsayina na matasa zan iya gyara masa ba tare da ransa ya baci ba, wanda zai rinka share mun kuka na a duk lokacin da wani abu ya damen ko ya ke shirin damuwa, wanda zai rinka kula da ni tamkar kwai. Irin auren da nake buri shi ne wanda za a yi shi a kwana biyu ta yadda ba zai zama takura da kowa ba sabida yanayin gari a yanzu da halin rayuwa, za a ci za a sha duk wani abun nishadi a sauke masa hakkinsa abu na lokaci daya ne ba wani bidi’a da kawo zancen malam ya ce, su ma malaman suna shagalin biki me dai. Zaman auren da nake son mu yi da shi ina son auren da zamu kasance cikin soyayya wanda zai rinka farantan a kullum ba iya lokacin da nake Amarya ba.
Daga Izzatu Khamis Jihar Kaduna
“Miji Mai Saukin Kai Nake So Wanda Zai Shirya ‘Party’ Kala Hudu A Aurenmu”
Ina son namiji me saukin kai ba irin namijin da zai rinka yi mun fada da tsayawa tamkar wata ‘yar sa ba, amma kuma ba na son Sokon namiji irin wanda zai tsaya sokoko mace na juya shi kamar a teburin me indomie, kuma me gemu nake so amma ba irin gemun Ustazai ba, Gemu na gayu irin na matasa me kyau. Auren mu ina so ya zamo an yi shagali sosai in da hali ayi party kamar kala hudu ko biyar, irin wanda za a kama hadaddun gurare tamkar bikin gidan manyan masu kudi. Rayuwar auren mu ina so ya zama cikin girmama juna da ma na iyayenmu dukka, mu kasance cikin masu gaskiya ban da ayyukan boye wanda Allah ya haramta.
Daga Hafiza Yusf Ahmad Jihar Jigawa
“Na Zabi Macen Da Ba Ruwanta Da Gantali”
Ina son mace kamila, wanda ta san me take, me kamun kai, wadda ba ruwanta da gantali, irin masu yawannan duk inda aka gayyace ta sai ta je bana so, gidan kawa gidan biki kullum tana hanya, bana son irin wannan macen. Shagalin biki ayi kowanne ba laifi muddin za mu samu farin ciki. Zaman Aure ba mu yi cikin kwanciyar hankali.
Daga Musa Boy Yaron Mama Jihar Katsina.
“Ba Na Son Mace Mai Tunanin Kasashen Waje”
Ba na son Mace me fadin rai, ina son mace mara buri da yawa, bana son mace me dogon burin da ba za a kaiwa gaci ba, bana son mace me tunanin kasashen waje, irin wadda komai nayi ba za ta yaba ba sabida burin da take ds take. Ina son ayi shagalin biki yadda ake yi wa kowa amma dai saffa-saffa.
Daga Al’ameen Gaddafi Jihar sokoto