Gwamnatin jihar Kebbi karkashin jagorancin Gwamna Nasir Idris tare da hadin gwiwar gidauniyar Nafisa Nasir Charity Development Foundation (NANAS) sun aurar da mata 300 a garin Birnin Kebbi tare da shawartar ma’auratan da su kasance masu sada zumunci da son juna.
Bikin wanda ya gudana a fadar Mai Martaba Sarkin Gwandu, Gidauniyar NANAS ce ta shirya wanda matar Gwamnan, Hajiya Nafisa Nasir Idris ta kafa.
- ‘Saurayin Da Muka Yi Alkawarin Aure Ya Fara Kula ‘Yan Mata Da Yawa, A Ba Ni Shawara’
- Kwamoti B Laori Ya Kaddamar Da Zauren Taro a Borrong, Demsa
Kakakin majalisar dokokin jihar Rt. Hon. Muhammad Usman Ankwe, shine ya wakilci gwamna a wajen bikin daurin auren inda ya bayyana cewa, za’a gudanar da irin wannan daurin auren lokaci-lokaci domin taimakawa marasa galihu maza da mata.
Dakta Nasir Idris ya ce, gwamnatinsa ta bayar da jimillar Naira miliyan 21 a matsayin sadaki ga matan da aka daura wa aure 300 da suka fito daga kananan hukumomin jihar 21, inda kowace amarya za ta samu sadaki Naira 70,000.
Ya kara da cewa, gwamnatinsa ta kuma samar da kayan daki da kayan abinci ga dukkan ma’auratan domin karfafa wa aurensu .
Haka kuma Gwamnan ya Kara da bayyana cewa an daura auren ne bayan tattaunawa da malaman addinin Musulunci bisa tsarin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi, wanda ya baiwa mabiyansa izinin yin mubayi’ar aure don amfanin al’umma da kuma haifar da zuriya masu albarka.
Daga karshe ya shawarci ma’aurata da su mutunta dokokin aure, yana mai cewa dole ne ango ya kare hakki da hakkokin matarsa, haka kuma matan su kasance masu aminci da goyon bayan mazajensu.
A nata jawabin, Uwargidan Gwamnan Jihar, Hajiya Nafisa Nasir Idris wadda ita ce ta kafa NANAS FOUNDATION, ta bayyana matukar jin dadinta ga mijin nata da ya ba ta tallafin kayan daki da kayan masarufi wanda ya sanya aka yi gagarumin bikin aure.