Gwamnatin Australiya ta soke matakin amincewa da birnin Kudus a matsayin babban birnin Israila.
A shekarar 2018 ne dai Firanministan lokacin Scott Morrison ya biye wa Amurka wurin daukar matakin.
To amma yanzu ma’aikatar harkokin wajen Australiya ta goge duk wata alama da ke nuna alaka da matakin a shafinta na internet.
Mai magana da yawun ma’aikatar ta ce ba za su amince da birnin Kudus a matsayin babban birnin Israila ba har sai an cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsakaninta da Falasdinu.
Daga: BBC Hausa