Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
Cinikin waje na kasar Sin ya ci gaba da samun bunkasa cikin sauri a watanni takwas na farkon shekarar 2026,...
Cinikin waje na kasar Sin ya ci gaba da samun bunkasa cikin sauri a watanni takwas na farkon shekarar 2026,...
Albarkacin kewayowar bikin baje kolin kasa da kasa na Sin na shekarar 2026, na cinikayyar samar da hidimomi ko CIFTIS,...
A yau Talata ne mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana cewa Sin ta...
Da safiyar yau Talata 8 ga wata ne mataimakin shugaban kasar Sin Han Zheng, ya halarci bikin bude taron tattaunawa...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya zanta ta wayar tarho da firaministan Birtaniya Andy Burnham a yau Talata. Yayin zantawar...
Kasashe 164 sun jefa kuri’ar nuna amincewa, a yayin da Amurka kadai ta ki, kuma da haka ne Majalisar Dinkin...
A gun taron manema labaru da ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gudanar a yau Litinin, ma’aikatar...
A yau Litinin ne mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana cewa mahukuntan gwamnatin...
A ranar 7 ga watan Satumba mai magana da yawun ma’aikatar harkokin waje kasar Sin Mao Ning ta jagoranci taron...
A makon da ya gabata ne hukumar kula da makamashi ta kasar Sin ta ce zuwa karshen watan Yulin bana, karfin tashoshin samar da lantarki daga hasken rana na kasar ya kai kilowatts biliyan 1.286, wanda a karon farko ya zarce na kwal. Wannan ya sa hasken rana ya zama hanya mafi girma ta samar da lantarki a kasar Sin. Kuma Lantarkin da aka samar daga hasken rana, ya dauki kaso 31.5 na yawan lantarkin da Sin take samarwa. Hakika kasar Sin ta mayar da makamashin hasken rana da ake ganin mai sarkakiya ne zuwa kashin bayan tsarin samar da makamashi a kasar, haka kuma makamashin da ake iya dogaro da shi. Har kullum kasar Sin na kara nuna wa duniya sabbin dabaru da manufofi da kwarewa, dake kara bayyana cewa, babu abun da ba zai yuwu ba, idan har aka jajirce aka samar da kyakkyawan tsari. Wannan ya alamta wata gagarumar nasara da Sin ta samu a kokarin da take yi na sauyawa zuwa amfani da makamashi mai tsafta da kuma rage fitar da hayakin Carbon mai gurbata muhalli. Bugu da kari, gagarumar nasara ce a shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15. Mummunan tasirin sauyin yanayi abu ne da ba ya bambance tsakanin kasashe ko al’ummomi, lamarin da ya sa shi zama wani batu mai muhimmanci da ya shafi daukacin mutanen duniya. Kasar Sin ta dauki batun tunkarar sauyin yanayi da muhimmanci. Don haka ta kowacce fuska tana iyakacin kokarin ganin ta lalubo hanyoyin da za ta rage fitar da hayaki mai guba domin bayar da gudunmawa ga kare muhalli da halittu da samar da duniya mai tsafta. Tabbas wannan nasara ba ita Sin ba ce kadai, ta duk duniya ce domin za ta kara ba kasashe kwarin gwiwar yin abun da ya kamata na ganin sun samar wa al’ummominsu makamashi mai tsafta da za a iya dogaro da shi, wanda kuma zai bayar da gudunmawa ga kokarin da ake yi na yaki da sauyin yanayi. Hakika ci gaban Sin a wannan bangare, yana nufin kasashe za su kara samun alfanu, domin zuwa yanzu, fasahar kasar Sin a wannan bangare na zama daya daga cikin wadanda ke kan gaba a duniya, inda zuwa yanzu ake gaggauta nazari da samar da ingantattun fasahohin samar da lantarki daga hasken rana da za a fara amfani da su a nan gaba. (Fa’iza Mustapha)
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.