Alkaluma da hukumar kula da gidajen waya ta kasar Sin ta samar sun yi nuni da cewa, a yayin bikin sabuwar shekara, yawan sakwannin kayayyakin da gidajen waya suka karba da kuma aikawa a kasar ya wuce biliyan 2.13.
Daga cikinsu, yawan sakwannin da aka karba ya kai biliyan 1.06, adadin ya karu da kaso 15.2% kwatankwacin makamancin lokacin bara, a yayin da yawan sakwannin da aka aika ya kai biliyan 1.07, wanda ya karu da kaso 11.5% bisa makamancin lokacin bara, lamarin da ya shaida farfadowar ayyukan yadda ya kamata.
Hukumar kula da gidajen waya ta kasar Sin ta ce, za ta yi iyakacin kokarin kiyaye gudanar da ayyukan gidajen waya yadda ya kamata, musamman ma ta fannin tura kayayyakin kiwon lafiya, da ma wadanda suka shafi rayuwar al’umma. (Lubabatu Lei)