Da misalin karfe 9:05 na safe (agogon Beijing), ranar Talata 7 ga watan Janairun 2025, wani sashe na jihar Xizang mai cin gashin kansa dake kudu maso yammacin kasar Sin ya tsinci kansa cikin ibtila’in girgizar kasa mai karfin maki 6.8, inda lamarin ya shafi a kalla mutane 60,000.
Idan irin wannan ibtila’i ya afku, hankula su kan karkata a kan kasar da abin ya afku domin a ga yadda za ta yi wajen saukakawa al’ummomin da abin ya shafa halin da suka tsinci kansu a ciki.
- Xi Ya Zanta Da Babban Jagoran Vietnam Da Shugaban Sri Lanka
- Karramawa: Ma’aikatan Kano Sun Yaba Wa Jagorancin Gwamna Abba Na Tausayi
Da yake kasar Sin tana fifita jama’a a gaba da komai, tabbas ba ta dauki lamarin da wasa ba, nan take Shugaba Xi Jinping ya umarci hada karfi da karfe daga dukkan bangarori wajen kai dauki ga mutanen da ibtila’in ya afkawa, har ma ya aike da mataimakin firaministan kasar, Zhang Guoqing zuwa yankin domin ya jagoranci ayyukan agaji.
Masu ayyukan ceto sun zage damtse tare da gwada tsere a tsakaninsu da kurewar lokaci wajen kakkafa tantuna na sake tsugunar da mutane a yankin, wanda a lokacin an yi hasashen yanayinsa na sanyi ya tsananta sosai.
Kazalika, masu ayyukan sa-kai daban-daban kowa ya nuna bajintar abin da zai iya gwargwadon hali. Daga cikinsu akwai wani mai shagon dafa taliya daga jihar Ningxia ta kabilar Hui mai cin gashin kansa, Wang Shengyun wanda ya yo tafiyar sama da kilomita 3,000 tare da abokansa zuwa yankin da abin ya shafa domin ba da agaji.
Wang Shengyun da abokansa sun taimaka wa al’ummar kauyen Gabu, da abincin da suka rika dafawa da kansu a kullum, irin su taliya, naman shanu da kayan marmari kamar su tuffa da kudinsu ya kai kimanin kudin Sin yuan 219,000, kwatankwacin dalar Amurka 30,000.
Jami’an ’yan sanda daga hukumar kula da shige da fice ta kasar Sin da ke yankin Xigaze a kalla 200 suka rika ceto mutanen da suka makale a baraguzai, tare da dabbobinsu da sauran kayayyakinsu masu amfani a kauyukan Yubai, Gabu da Zacun da ke birnin Changsuo. Saboda yawan aikin da suke yi da kyar suka rika samun hutu. Wani babban jami’i daga ofishinsu na Nyima ya ce, idan aiki ya yawaita a wani kauye ko jami’an can sun gaji ainun, su kan kwashi jami’ai daga yankunan da aikin ke da sauki zuwa can.
Wasu mazauna kauyukan da abin ya faru dai, sun tabbatar da cewa sun samu dauki daga ’yan sanda cikin minti 30 kacal da afkuwar ibtila’in.
Ma’aikatar kudi da ta ba da agajin gaggawa ta kasar Sin sun fitar da kudin Sin yuan miliyan 100, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 13.9 don tallafa wa ayyukan agaji a jihar ta Xizang.
Haka nan, domin sake mayar da al’ummomin da abin ya shafa cikin hayyacinsu, ma’aikatar kudi ta kasar Sin ta sake kebe kudin Sin yuan miliyan 80 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 11, domin farfadi da aikin gona a jihar ta Xizang. (Abdulrazaq Yahuza Jere)