Rundunar ‘yansandan Jihar Adamawa ta musanta rahoton da ke cewa wasu ‘yan fashi da makami sun kai wa ayarin motocin Gwamna Ahmadu Fintiri hari a Jihar Taraba kwanan nan.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, Moris Danwambo, ya bayyana a ranar Alhamis cewa rahotannin da aka wallafa a kafafen sada zumunta kan harin ba gaskiya ba ne, kuma labari ne na karya.
- Fiye Da Kaso 80 Na Kamfanonin Sin Sun Fadada Zuba Jari A Waje A 2024
- Fiye Da Kaso 80 Na Kamfanonin Sin Sun Fadada Zuba Jari A Waje A 2024
A cewarsa, a ranar 19 ga watan Disamba, wata mota daga cikin motocin jami’an tsaro da ke cikin ayarin gwamnan, yayin da suke dawowa daga Taraba, ta yi karo da shingen da ‘yan fashi suka kafa.
Ya bayyana cewa, a tsarin zirga-zirgar manyan baki (VIP), motar jami’an tsaro ce ke gaba. Da suka iso wurin da lamarin ya faru, shingen ya hana matafiya wucewa, har sai da suka tsaya a hanya.
Jami’an tsaron da ke cikin ayarin sun yi gaggawar daukar mataki, inda suka tarwatsa ‘yan fashin tare da bude hanya domin sauran matafiya su ci gaba da tafiyarsu lafiya.
Kwamishinan ya yabawa jajircewar jami’an tsaro kan aikin nasu, tare da yin kira ga masu amfani da kafafen sada zumunta da su tabbatar da gaskiyar kowanne labari kafin wallafa shi.