Tsohon gwamnan Jihar Abia, Orji Uzor Kalu, ya karyata rahotonnin da kafafen yaɗa labarai suke yadawa na cewa an nada shi darakta-janar na gangamin yakin kamfen din Ahmad Lawan na neman Shugabancin Kasa.
Rahotonnin da aka yada a ranar Alhamis sun nuna cewa an nada ni (Chief whip) na Majalisar Dattawa da wasu masu ruwa da tsaki a kwamitin yakin neman zaben Ahmad Lawan.
Da ya ke maida martani kan wannan batun a wata sanarwar da ya fitar Kuma ya raba wa manema labarai a daren ranar Alhamis, ya karyata rahoton gaba daya, ya ce jerin sunayen kwamitin yakin zaben da ake yadawa babu gaskiya a cikinsa.
Kalu ya roki al’umma da su yi watsi da rahotonnin na cewa cewa an nadashi daraktan yakin kamfen din Ahmad Lawan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp