Ƙungiyar mawaƙan Hausa mai suna Murya Daya, ta barranta kanta daga kalaman da mawaƙin siyasa, Dauda Kahutu Rarara, ya yi a baya bayan nan.
Wanda ya soki tsohon shugaban ƙasar Nigeria, Muhammadu Buhari, ya kuma bayyana wa gwamnatin shugaba, Bola Ahmed Tinubu, cewar ba zai yi hakuri kamar yadda ya yi a gwamnatin Buhari ba.
- Kuskure Ne A Ɗauka RARARA Ba Kowan Komi Ba Ne – Farfesa Malumfashi
- ‘Yan Nijeriya Za Su Iya Tara Min Kudi Don Yi Wa Tinubu Waka Saboda Kaunarsa -Mawaki Rarara
Shugabannin ƙungiyar da suka hada da Ali Isa Jita da El-Mu’az Kaduna da Ado Gwanja da sauransu, sun ce bai kamata mutane su yi wa mawaƙan kuɗin Goro ba cewa su kamar Karnuka ne.
Bai kamata don wani daga cikinmu ya yi kuskure sai a dauka cewar duk haka muke ba, ya kamata a mana adalci. Cewar mawakan.
Ƙungiyar ta bayyana haka ne a wani taron manema labarai da ta kira, inda ta jaddada cewa, mawaƙa za su ci gaba da girmama shugabanni na kan kujerar mulki da wadanda suka sauka.