Hukumar kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Ƙasa NPA, ta jaddada cewa, tsarin “Call-up system” da ta ƙirƙiro da shi, domin lura da zirga-zirgar manyan motocin da ke shige da fice a Tashar Jirgin Ruwa, na nan daram dam
NPA ta bayyana hakan ne, ta bakin Babban Manajan Huɗɗa da Jama’a da Samar da Bayanai na Hukumar Mista Ikechukwu Onyemekara.
Ogunojemite ya sanar da hakan ne, wata hira da Jaridar PUNCH yi da shi, ta wayar Tarho, a ranar Litinin.
Ya sanar da hakan ne, a matsayin mayar da martani, kan buƙatar da ƙungiyar ƙwararu ta Afirka reshen ƙasar nan da ke jigilar kaya zuwa cikin Tashar suka yi, wato AAPFFLN na soke wannan tsarin, da aka gabatar a Tashar Jiragen Ruwa ta Onne.
- Tinubu Ya Amince A Fara Aikin Tashoshin Jiragen Ruwa Na Apapa Da Kalaba Da Fatakwal Da Warri — NPA
- Yadda Ɗantsoho Ya Mayar Da Hankali Wajen Farafaɗo Da Martaba Da Ƙimar NPA
Sun gabatar da buƙatar soke tsarin ne, a wata wasiƙa da suka rubutawa Shugaban Hukumar ta NPA Dakta Abubakar Ɗantsoho.
Shugaban ƙungiyar ta ƙasa, Frank Ogunojemite, ne ya sanya rattaba hannunsa a wasiƙar kamar yadda Jaridar PUNCH, ta samu kwafinta.
Shugaba ya bayyana cewa, ya kafa hujjar buƙatar soke tsarin, kan ƙalubalen da take fuskanta, na kashe kuɗaɗe masu yawa, musamman wajen safarar mayan Kwantainonin da ake shigoa da su daga ƙasashen da ke a Afirka ta Yamma
Ya ce, wannan tsarin ya sanya a yanzu, ana yiwa masu safarar kaya zuwa cikin Tashar wani sabon cajin kuɗi da kuma jinkirin da suke samu, wajen shigar da kayan zuwa cikin Tashar.
Ogunojemite ya buƙaci Hukumar da ta tabbatar da wanzar da tsarin a matsayin na bai ɗaya a ɗaukacin Tashishin Jiragen Ruwan ƙasar.
“Muna gabatar da wannan buƙatar ce, domin mun yi amanna da cewa, a ƙarƙashin shuganacin shugaban Hukumar zai ci gaba da yin adalci da kuma tabbatar da ana bin ƙa’ida da kuma yin dubi ga lamarin ci gaban ƙasar nan, kan abinda ya shafi tafiyar da harkokin Jiragen Ruwan ƙasar,” Inji Ogunojemite.
“A shirye muke domin yin tattaunawa da Hukumar da kuma sauran hukomin da abin ya shafa domin a lalubo da mafita, kan wannan buƙatar ta mu.” A cewar shugaban.
Sai dai, a martanin da Onyemekara ya jaddada cewa, babu gudu ba bu ja da baya na dakatar da wannan tsarin.














