Wani lauya kuma masani a harkokin wasanni, Rayond Hack, ya bayyana shakku kan yiwuwar Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) ta kakabawa Afirka ta Kudu hukuncin cire mata maki uku, duk da zargin saka ɗan wasa da bai cancanta ba a gasar neman gurbin shiga cin Kofin Duniya. Ana zargin Afirka ta Kudu da saka ɗan wasan tsakiyarta, Teboho Mokoena, duk da cewa yana da katin gargadi biyu.
Hack ya ce abin da ya sa ake ganin FIFA na jan kafa shi ne saboda tawagar Lesotho, wacce lamarin ya shafa kai tsaye, ba ta gabatar da ƙorafi ko neman a binciki Afirka ta Kudu ba. Wannan, a cewarsa, na iya zama dalilin da ya sa hukumar ba ta gaggauta yanke hukunci ba.
- An Fara Jigila Kai Tsaye Daga Lardin Zhejiang Na Sin Zuwa Nahiyar Afrika
- Ilimin Fasahar Zamani Dama Ce Ta Samun Kyakkyawar Makoma A Afrika
Sai dai hakan bai hana masoya kwallon kafa da ƙasashen da ke cikin rukuni C nuna mamaki ba, domin sun bukaci FIFA ta bayyana matsayarta da gaggawa. A cewarsu, hukuncin kan batun Mokoena na da matuƙar muhimmanci ga adalcin gasar, musamman ganin cewa sauran ƙasashe kamar Nijeriya, Benin, Rwanda, Zimbabwe da Lesotho suna fafatawa a rukuni ɗaya da Afirka ta Kudu.
Idan har FIFA ta yanke hukuncin cire maki uku daga Afirka ta Kudu, hakan na iya sauya lissafi a teburin rukuni C, wanda zai shafi damar da kowace ƙasa ke da ita wajen samun tikitin zuwa gasar cin Kofin Duniya ta 2026. Sai dai a halin yanzu, hukumar ta ci gaba da yin shiru kan lamarin, lamarin da ke ƙara haifar da ce-ce-ku-ce tsakanin masu ruwa da tsaki a harkar kwal
lon kafa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp