Gwamnatin Jihar Katsina, ta bayyana cewa ba ta da hannu a wani zaman sulhu da ake zargin an yi da ‘yan bindiga, duk da rahotannin da ke cewa an cimma yarjejeniyar sulhu da shugabannin ‘yan bindiga a Ƙaramar Hukumar Batsari.
Kakakin Gwamnati kuma Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na Jihar Katsina, Dokta Bala Salisu ne, ya shaidawa Daily Trust cewa gwamnatin jihar ta tsaya kan matsayinta na ƙin yin sulhu da ‘yan bindiga.
- Trump Zai Fuskanci Tirjiya A Duniya, Ba Soyayya Ba – Shehu Sani
- Yaƙin Gaza: Falasɗinawa Sun Fara Neman ‘Yan Uwansu Da Suka Ɓace A Baraguzan Gine-gine
Duk da haka, ya ce gwamnati za ta karɓi duk wani da ya yanke shawarar ajiye makamansa.
“Ba mu da hannu a kowace yarjejeniya ta zaman lafiya.
“Matsayin gwamnati yana nan a bayyane: duk wanda ya bar tashin hankali kuma ya ajiye makamai za mu yi la’akari da shi.
“Amma ba za mu nemi ‘yan bindiga don yin sulhu ba,” in ji Dokta Salisu.
Rahotanni sun ce an yi wata ganawar zaman lafiya a ranar Lahadi a ƙauyen Kofa, kusa da garin Batsari, tare da jagorancin manyan jami’an soji, DSS, sarakunan gargajiya, da mazauna yankin.
Wani mazaunin yankin da ya halarci ganawar ya ce ‘yan bindigar sun yi alƙawarin daina kai wa al’umma hare-hare.
Sannan za su saki mutanen da suka yi garkuwa da su tare da miƙa makamai.
“Sun nemi a ba su damar shiga cikin al’umma lafiya, kuma wannan zaman an ce shi ne farkon sulhun,” in ji mazaunin.
An ce manyan shugabannin ‘yan bindiga kamar Lamu Saudo, Abdulhamid Dan Da, Umar Black, da Abu Radda sun miƙa makamansu tare da sakin waɗanda suka yi garkuwa da su a yayin taron.
Majiyoyin soji sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun miƙa wuya ne sakamakon matsin lamba da hare-haren sojoji ke ci gaba da kai musu, wanda ya sa ba su da wani zaɓi illa neman zaman lafiya.
Kakakin Rundunar Sojojin ta 17, Laftanar Lawal, ya tabbatar da wannan lamari, inda ya bayyana cewa ci gaba da matsin lambar jami’an tsaro ne ya sa ‘yan bindigar suka miƙa wuya.