Jam’iyyar adawa ta ADC ta ce iƙirarin gwamnati cewa matakan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne suka kawo sauƙin farashin kayan abinci ba gaskiya ba ne.
Jam’iyyar ta zargi gwamnati da yaudarar ‘yan ƙasa da labarin karya, tana mai cewa abin da ake ya kawo sauƙin abinci a kasuwa ba ƙoƙarin manufofin gwamnati ba ne.
- Firaministan Sin Ya Yi Kira Da A Kara Bude Kofa Da Karfafa Daidaita Dabarun Samar Da Ci Gaba
- Masanan Kasar Sin Da Afirka Sun Hada Karfi Da Karfe Don Habaka Samun Wadatar Abinci Da Zamanantar Da Aikin Gona
Kakakin jam’iyyar, Faisal Kabiru, ya ce farashin kayan noman gida ya faɗi ne saboda tsoro da rashin daidaito a kasuwa, ba wai saboda wata nasarar gwamnati ba.
“Manoma suna kashe kuɗi masu yawa wajen noma, amma gwamnati ta karya farashin kayan su, yayin da kayan da ake shigowa da su daga waje ke ƙara tsada,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa manoma da dama yanzu ba su da jarin da za su ci gaba da noma saboda rage farashin kayan da suka noma.
Sai dai gwamnatin Tinubu ta mayar da martani, tana cewa jam’iyyar ADC kawai tana adawa ne da nasarorin da gwamnati ke samu.
Hadimin shugaban kasa, Abdulaziz Abdulaziz, ya ce: “Da farko ‘yan adawa suna ƙorafi cewa abinci ya yi tsada. Yanzu da gwamnati ta ɗauki matakai don rage tsada, sai kuma suke kuka.”
A watan Satumba 2025, Shugaba Tinubu ya umarci kwamiti na musamman na gwamnati da ya ɗauki matakan gaggawa don rage tsadar abinci a faɗin ƙasar nan.
Duk da haka, wasu manoma na kukan cewa matakan sun jawo musu asara saboda tsadar kayan noman da suke amfani da su.














