Sanata Oluremi Tinubu, ta ce bai kamata a zargi mijinta, Bola Tinubu ba, kan tabarbarewar tattalin arziki da ake fama da shi a Nijeriya.
‘Yan Nijeriya dai na cikin hali na matsin tattalin arziki tun bayan cire tallafin man fetur wanda ya sauya farashin man fetur daga Naira 198 zuwa Naira 1,030.
- Majalisa Ta Amince Jami’an Kiyaye Haɗurra Su Riƙe Bindiga
- Yawan Kwangilolin Da Kamfanonin Kera Jiragen Ruwa Dake Aiki Da Makamashi Mai Tsabta Na Sin Suka Samu Ya Kai Kashi 70% Bisa Na Duniya
Sai dai a lokacin da take magana a fadar Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi, a ranar Alhamis, Uwargidan shugaban kasar ta ce, gwamnatin Tinubu har yanzu bata gama murmurewa ba.
Uwargidan shugaban kasar, ta je garin Ife ne domin kaddamar da dakunan kwanan dalibai da wata hanya mai tsawon kilomita 2.7 da Ooni na Ife ya bai wa Jami’ar Obafemi Awolowo, (OAU), wanda aka sanya sunanta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp