Kungiyar ‘Yan Jarida ta Nijeriya (NUJ), bangaren wakilan gidajen jaridun kasar nan da ke a Jihar Kebbi, sun yi watsi da zaben mambobinta guda uku kacal da za su rika daukar rahotannin Gwamna Nasir Idris a gidan gwamnati da ke Birnin Kebbi.
Hakan na kunshe ne a wata takardar sanarwa da aka raba wa manema labarai da shugabancin kungiyar tasu ta jihar mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar Alhaji El-Yukub Usman da sakatarenta Ibrahim Bello a Birnin Kebbi.
Wannan kin amincewa ya biyo bayan wani taron tattaunawa da aka yi a Birnin Kebbi ranar Talata tsakanin mukaddashin Babban sakataren gidan gwamnati, Alhaji Ibrahim Saraki; mukaddashin Babban sakatare na hidindimun gwamna, Alhaji Sagir Mahe, da mai ba da shawara na musamman kan harkokin yada labarai ga Gwamna Nasir Idris, Malam Yahaya Sarki.
Sauran wadanda suka halarci taron tattaunawar sun hada da, Alhaji Aliyu Bandado, mai bai wa gwamna Idris shawara kan sabbin kafafen yada labarai kuma MC ga Gwamna, Alhaji Faruk Bello-Birnin Kebbi.
A ganawar tasu, sun cimma matsayar cewa gwamnan ya ba da umarnin cewa ba ya son ganin sama da mambobin ‘yan jarida uku da za su rika daukar labarun fadar gwamnatinsa.
Da yake mayar da martani kan wannan, Shugaban kungiyar, Alhaji El-Yakubu Usman-Dabai, ya bayyana wannan matakin a matsayin ‘mara amfani’ ga bangaren inganta ayyukan gwamnatin Kebbi, da kuma aikin jarida.
“A halin yanzu muna da mambobi sama da 18, Kuma kowani wakili suna da salon daukar labari daban-daban na cikin gida, masu wakiltar kafafen yada labarai daban-daban a ciki da wajen Nijeriya, bai dace ba da rashin da’a a ba da dama ga mambobi uku kacal.
“Ka da jami’an gwamnati su manta da cewa, muna da wakilan talabijin da rediyo da jaridu da kafafen yada labarai na yanar gizo wadanda salon gidajensu ya bambanta da juna.
“Lokacin da kuka dauki jaridu don yin ayyukanku, kuna tauye wa sauran ‘yan jarida hakkinsu na tsarin mulki na sanar da al’ummar Kebbi game da ayyukan alheri da gwamnan yake yi.
“Muna da mutanen da ke zaune a wurare masu nisa da ke dogaro da rediyo da talabijin kawai don samun bayanai game da manufofin gwamnatinsu da shirye-shiryen gwamnatinsu a jihar,” in ji shi.
Usman-Dabai ya bukaci jami’an da abin ya shafa da su janye matakin da suka dauka, kasancewar ‘yan jarida abokan aikinsu ne.