ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ba Mu Amince Da Ware Mutum Uku Kacal Su Dauki Rahotannin Gwamnan Kebbi Ba – ‘Yan Jarida

by Umar Faruk
3 years ago
'Yan jarida

LABARAI MASU NASABA

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Kungiyar ‘Yan Jarida ta Nijeriya (NUJ), bangaren wakilan gidajen jaridun kasar nan da ke a Jihar Kebbi, sun yi watsi da zaben mambobinta guda uku kacal da za su rika daukar rahotannin Gwamna Nasir Idris a gidan gwamnati da ke Birnin Kebbi.
Hakan na kunshe ne a wata takardar sanarwa da aka raba wa manema labarai da shugabancin kungiyar tasu ta jihar mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar Alhaji El-Yukub Usman da sakatarenta Ibrahim Bello a Birnin Kebbi.
  • Ana Kokarin Rantsar Da ‘Yan APC 16 A Majalisar Filato Ta Barauniyar Hanya – Gwamnatin Jihar
Wannan kin amincewa ya biyo bayan wani taron tattaunawa da aka yi a Birnin Kebbi ranar Talata tsakanin mukaddashin Babban sakataren gidan gwamnati, Alhaji Ibrahim Saraki;  mukaddashin Babban sakatare na hidindimun gwamna, Alhaji Sagir Mahe, da mai ba da shawara na musamman kan harkokin yada labarai ga Gwamna Nasir Idris, Malam Yahaya Sarki.
Sauran wadanda suka halarci taron tattaunawar sun hada da, Alhaji Aliyu Bandado, mai bai wa gwamna Idris shawara kan sabbin kafafen yada labarai kuma MC ga Gwamna, Alhaji Faruk Bello-Birnin Kebbi.
A ganawar tasu, sun cimma matsayar cewa gwamnan ya ba da umarnin cewa ba ya son ganin sama da mambobin ‘yan jarida uku da za su rika daukar labarun fadar gwamnatinsa.
Da yake mayar da martani kan wannan, Shugaban kungiyar, Alhaji El-Yakubu Usman-Dabai, ya bayyana wannan matakin a matsayin ‘mara amfani’ ga bangaren inganta ayyukan gwamnatin Kebbi, da kuma aikin jarida.
“A halin yanzu  muna da mambobi sama da 18, Kuma kowani wakili suna da salon daukar labari daban-daban na cikin gida, masu wakiltar kafafen yada labarai daban-daban a ciki da wajen Nijeriya, bai dace ba da rashin da’a a ba da dama ga mambobi uku kacal.
“Ka da jami’an gwamnati su manta da cewa, muna da wakilan talabijin da rediyo da jaridu da kafafen yada labarai na yanar gizo wadanda salon gidajensu ya bambanta da juna.
“Lokacin da kuka dauki jaridu don yin ayyukanku, kuna tauye wa sauran ‘yan jarida hakkinsu na tsarin mulki na sanar da al’ummar Kebbi game da ayyukan alheri da gwamnan yake yi.
“Muna da mutanen da ke zaune a wurare masu nisa da ke dogaro da rediyo da talabijin kawai don samun bayanai game da manufofin gwamnatinsu da shirye-shiryen gwamnatinsu a jihar,” in ji shi.
Usman-Dabai ya bukaci jami’an da abin ya shafa da su janye matakin da suka dauka, kasancewar ‘yan jarida abokan aikinsu ne.
'Yan jarida
Umar Faruk
+ postsBio
  • Umar Faruk
    https://hausa.leadership.ng/author/umar-faruk/
    Gwamnatin Kebbi Ta Amince Da ₦2.07bn Alawus-alawus Ga Ma’aikatan Manyan Makarantu
  • Umar Faruk
    https://hausa.leadership.ng/author/umar-faruk/
    Gwamnan Kebbi Ya Maye Gurbin Mataimakinsa Da Ibrahim Augie A Zaɓen 2027
  • Umar Faruk
    https://hausa.leadership.ng/author/umar-faruk/
    Matashi Ya Shiga Hannu Kan Zargin Wulaƙanta Alƙur’ani A Kebbi
  • Umar Faruk
    https://hausa.leadership.ng/author/umar-faruk/
    Gwamnan Kebbi Ya Miƙa Yara 5 Da Aka Ceto Daga Hannun Masu Safarar Mutane Ga Iyayensu
ADVERTISEMENT

MASU ALAKA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja
Labarai

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Next Post
Bai Kamata Jama’a Su Tsorata Da Bullar Zazzabin Lassa A Adamawa Ba – Kwamishinan Lafiya

Bai Kamata Jama'a Su Tsorata Da Bullar Zazzabin Lassa A Adamawa Ba - Kwamishinan Lafiya

LABARAI MASU NASABA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.