• English
  • Business News
Sunday, November 2, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ba Mu Da Alaƙa Da Duk Wata Talla Ta Zambatar Al’umma – Rundunar Soji 

by Muh'd Shafi'u Saleh
2 years ago
Soji

Rundunar sojin Nijeriya ta 23 da ke Yola, ta gargadi jama’a game da wata sanarwar talla da ke yawo a kafofin sada-zumunta, kan wani taron bayar da agaji mai taken ‘A 3 Day Charity Exercise/10km Trek 2024’.

Rundunar ta ce, sanarwar ta yi ikirarin gudanar da bukin cika shekaru 25, na hidimar jin kai na kungiyar matan sojojin Nijeriya (NAOWA), da akace za’a gudanar da taron a ofishin jami’an soji da ke Yola daga ranar 8 zuwa 11 ga Fabrairu, 2024.

  • Rundunar Soji Ta Kudancin Sin Ta Gudanar Da Ayyukan Sintiri Na Dakarun Sojin Ruwa Da Na Sama A Tekun Kudancin Kasar
  • ‘Yansanda Sun Kama Dan Bindiga, Sun Ki Karbar Cin Hancin Miliyan 8 A Taraba

Cikin sanarwar da mukaddashin jami’in hulda da jama’a na rundunar sojin da ke Yola, Laftanar Princewill Odoemenam, ya aikewa manema labarai, ta ci gaba da cewa “tallar ana zargin wani mutum mai suna AB Gofai AFOBREF da ya sanya wa hannu, ya ce shi ne Kwamanda, tare da bayar da lambar waya (08123497002).

“Tallar ta bukaci jama’a da su biya kudin talla ta Firstmonie Wallet da Palmpay asusun mai lamba 8132843616, a karkashinsa ansa sunan asusu Captain Jacub BD” inji sanarwar.

Rundunar ta ce “ba tare da wata shakka ba, ba mu da alaka da wannan sanarwa, bamu san wani Kwamanda mai suna AB Gofai ba, kuma bamu da duk wata alaka da wani mutum da aka ce Captain Jacub BD a cikin Runduna ta 23.

LABARAI MASU NASABA

A Kan Wa Trump Ke Son Kaddamar Da Hari a Najeriya?

Maganin Nankarwa (3)

“Muna gargadin jama’a sosai game da biyan duk wani kudi ga asusun da aka ambata, bugu da kari, rundunar soji ta 23, ta jaddada cewa babu irin wannan shirin gudanar da biki kamar yadda aka bayyana a sama.

“Mun nisanta kan mu da wannan tallar na bogi, tare da shawartar jama’a da su yi taka-tsan-tsan da kaurace wa duk wata kiraye-kiraye na talla, ko daukar nauyin gudanar da wani taron karya da aka ambata a sama.

“Rundunar Sojin Nijeriya, ta dauki al’amuran zamba da mazambata da muhimmanci, tana karfafa wa jama’a gwiwa da su kai rahoton duk wani abin da suke zargi ga hukumomin da suka dace” inji Princewill.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

A Kan Wa Trump Ke Son Kaddamar Da Hari a Najeriya?
Ra'ayi Riga

A Kan Wa Trump Ke Son Kaddamar Da Hari a Najeriya?

November 2, 2025
Maganin Nankarwa (3)
Labarai

Maganin Nankarwa (3)

November 2, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP
Labarai

Dalilin Da Ya Sa Hukumar NIWA Ta Fara Gyaran Hanyoyin Ruwa A Jihar Legas

November 2, 2025
Next Post
AFCON 2023: Hasashe Ya Nuna Nijeriya Ce Za Ta Lashe Gasar Cin Kofin Afirika Ta Bana

Tsokaci Dangane Da Juyin Mulki A Nahiyar Afirka

Tsokaci Dangane Da Juyin Mulki A Nahiyar Afirka

November 2, 2025
Barazanar Amurka Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya: Tinubu Da Trump Za Su Gana Kwanan Nan — Bwala

Barazanar Amurka Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya: Tinubu Da Trump Za Su Gana Kwanan Nan — Bwala

November 2, 2025
Yaya Da Kani Sun Mutu A Cikin Ramin Masai A Kano

An Kashe Mutum 3 Yayin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Hari Kan Iyakokin Kano

November 2, 2025
Dalilin Gwamnatin Jihar Kuros Riba Na Raba Wa Manoma Taraktoci

Dalilin Gwamnatin Jihar Kuros Riba Na Raba Wa Manoma Taraktoci

November 2, 2025
Yadda Ƴan Mata Ke Kashe Kuɗaɗe Wajen Yi Wa Samarinsu Hidima

Yadda Ƴan Mata Ke Kashe Kuɗaɗe Wajen Yi Wa Samarinsu Hidima

November 1, 2025
Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori

Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori

November 1, 2025
Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna

Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna

November 1, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.