A jiya Laraba ne jam’iyyar PDP ta bayyana cewa ba za ta shiga tsarin siyan kuri’u ba, inda ta ce tana tsammanin samun kuri’un matasa miliyan 10 a zaben 2023 mai zuwa.
Jam’iyyar ta bayyana hakan ne a lokacin da take gangamin rangadin wayar da kan jama’a na karbar katin zabe na dindindin (PVC) gabanin zaben 2023.
Shugabannin jam’iyyar da suka hada da sakataren yada labarai na kasa, Debo Ologunagba; Shugabar mata ta kasa, Farfesa Stella Effa-Attoe, da shugaban matasan jam’iyyar na kasa, Muhammed Suleiman ne suka jagoranci gangamin a manyan titunan Abuja.
A lokacin gangamin wayar da kan masu kada Kuri’a don samun katin zaben su, shugaban matasan jam’iyyar na kasa, Muhammed Suleiman, ya ce, “Muna bikon matasa miliyan 10 kuma muna da yakini za su zabi PDP a 2023.”
Ya kara da cewa sun yanke shawarar fara wannan rangadin na wayar da kan jama’a ne domin su fito su yi rajista da kuma samun katin zabe na dindindin (PVC), hakan ita ce kadai hanyar da za a iya samun shugabanci nagari a Nijeriya.