Assalamu alaikum. Allah ya taimaki malam, ina tsananin son wata yarinya, idona duk ya rufe a kanta, amma ita kuma ba ta so na, na ransa yadda zan yi saboda zankwadediya ce, son kowa kin wanda ya rasa, ba na iya bacci saboda tunaninta, a ba ni shawara. Na gode
Wa alaikum assalam. To, dan’uwa ka nemi zabin Allah a duka lamuranka, “Allah yana cewa : “Ya kusanta ku ki abu, amma kuma alkairi ne gare ku, za kuma ku iya son abu, amma sharri ne a gare ku” Bakara aya ta 216.
Wannan aya ta kunshi sirrirrika da yawa, saboda duk lokacin da bawa ya san cewa, abu mai kyau, yana iya zuwa da mara kyau, sannan mara kyau yana iya zuwa da mai kyau, wannan zai sa ba zai aminta daga cewa musiba za ta iya samun sa ta hanyar farin ciki ko akasin haka ba, saboda ba shi da ilimin karshen lamura, Allah kuma ya san abin da bawa bai sani ba.
Wannan zai wajabtawa bawa abubuwa kamar haka:
1. Babu abin da ya fi ga bawa fiye da ya aikata abin da Ubangijinsa ya umarce shi, ko da kuwa da wahala, saboda karshen aikinsa zai zama farin ciki da kuma annashuwa.
2. Ya wajaba ya bar aikata sabo, saboda karshensa musifu ne masu yawa, ko da kuwa farkonsa akwai annashuwa.
3. Yana da kyau bawa ya mika lamuransa zuwa wanda ya san makomar al’amura wato Allah, ya kuma yarda da abin da ya zabar masa.
4. Kar ya roki Ubangijinsa abin da ba shi da ilimi a kai, zai iya yiwuwa ya hallaka ko ya cutu, idan aka ba shi wannan abin, kamata ya yi ya roki ubangijinsa ya zaba masa.
5. Duk lokacin da bawa ya nemi zabin Allah, hakan zai hutar da shi daga yawan tunani, na abin da zai aikata.
Don neman karin bayani duba AL- FAWA’ID 246
Allah ne mafi sani.