Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya ce ko kadan baya kewar zaman da ya yi a fadar shugaban kasa.
Buhari ya bayyana hakan ne lokacin da yake tattaunawa da gidan talabijin na kasa (NTA), lokacin da yake amsa tambayan kan abun da yake kewa daga tsohon ofishinsa na shugaban kasa.
- Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Da Nasarar Abdullahi Sule Bayan Kotun Sauraron Zabe Ta Tsigeshi
- Kano: Kotun Daukaka Kara Ta Bukace Lauyoyin Su Mayar Da Kwafin Takardun Shari’ar
Watanni kafin ya mika mulki, Buhari ya ce ba zai taba yin kewar zamansa shugaban Nijeriya ba, saboda ya yi iya bakin kokarin da zai yi wa ‘yan Nijeriya.
“Na tabbata na yi iya bakin kokarina, amma duk da haka kwazona bai is aba. Ina mamaki yadda zan yi kewar barina ofishin shugaban kasa. Ina tunanin ana tursasa ni,” in ji shi.
Wannan it ace tattaunawar farko da Buhari ya yi tun bayan da ya bar mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023.