ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Abin Da APC Za Ta Yi Da Rinjayen Kashi Biyu Bisa Uku A Majalisar Tarayya

by Yusuf Shuaibu
10 months ago
APC

Jam’iyyar APC ta samun rinjaye kashi biyu bisa uku a zauren majalisar wakilai bayan sauya shekar wasu ‘yan majalisar shida a ranar Alhamis, makonni kadan bayan samun irin wannan rinjayen a zauren majalisar dattawa.

Mambobi biyar na jam’iyyar PDP daga Jihar Inugu da dan majalisar dokoki daya na jam’iyyar LP daga Jihar Filato sun sanar da sauya sheka zuwa APC a lokacin zaman majalisa, wanda hakan ya kara karfin adadin mambobin jam’iyyar mai mulki a majalisar wakilai.

  • Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka
  • Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

Iyakacin rinjaye na kashi biyu bisa uku a majalisar wakilai da ke da mambobi 360 shi ne 240. Tare da sabbin sauye-sauyen ‘yan majalisa, APC yanzu tana da kujeru 243, yayin da PDP ta sauka zuwa 72. LP tana da kujeru 21, NNPP na da 15, APGA na da 5, ADC na da 1, SDP na da 2, sai kuma YPP na da 1.

ADVERTISEMENT

A zauren majalisar dattawa kuwa, APC ta riga ta samu irin wannan rinjayen tun a farkon tsakiyar wannan shekara.

Tun bayan kaddamar da majalisar tarayya ta 10 a watan Yunin 2023, APC na da kujeru 175 a majalisa, yayin da jam’iyyun adawa da aka hada gaba daya suka rike 182, wanda hakan ya ba su karamin rinjaye a wancan lokacin. Duk da haka, yawan sauya sheka da aka samu a cikin shekarar da ta gabata ya juya wannan lamari, yana karfafa rinjayen APC a duka majalisar guda biyu, a daidai lokacin da ‘yan majalisa ke sake tsara kansu kafin zaben 2027.

LABARAI MASU NASABA

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta

Samun rinjayen da APC ta yi na kaso biyu bisa uku a dakunan majalisa biyu yana da babban tasiri ga tsara dokoki, gyaran kundin tsarin mulki da kuma tsarin iko a cikin majalisar tarayya.

Dangane da gyare-gyaren kundin tsarin mulki, bisa sashe na 9 (2) da (3) na kundin tsarin mulki na 1999 (kamar yadda aka gyara), kowane kudiri da ke neman canza kundin tsarin mulki dole ne ya sami goyon bayan akalla kashi biyu cikin uku na dukkan mambobin kowanne majalisa kuma a tabbatar da kashi biyu cikin uku na majalisun jihohi 36 (jihohi 24).

Bisa adadin mambobinta a yanzu, cikin sauki APC na iya tura dokokin gyaran kundin tsarin mulki a majalisar tarayya, ko da yake amincewar matakin jiha na ci gaba da kasancewa wani shinge da ake bukata.

Haka kuma, dangane da tsige shugaban kasa ko mataimakinsa, sashe na 143 (4) da (9) na kundin tsarin mulki na bukatar rinjaye na kaso biyu bisa uku a dukkan majalisu biyu don cire shugaban kasa ko mataimakin shugaban kasa saboda aikata laifuka masu tsanani. A hali ynzu dai, jam’iyyar APC tana iya kare shugaban kasa daga kowace yunkurin tsige shi, domin ‘yan majalisa na adawa ba su da yawan da za su iya yunkurin tsige shugaban kasa ko mataimakinsa.

Kazalika, dangane da cire duk wani babbab jami’an gwamntin kuwa, sashe na 50 (2)(c) da 92 (2)(c) na kundin tsarin mulki sun tanadi cewa shugaban majalisar dattawa da shugaban majalisar wakilai ko mataimakansu za a iya cire su ne kawai da rinjaye na kashi biyu cikin uku na majalisunsu. Wannan yana nufin cewa a halin yanzu manyan jami’an gwamnati na iya samun goyon bayan rinjayen APC mai yawa wajen samun kariya daga kokarin korarsu daga mukamansu.

Idan za a ayyanawa ko tsawaita dokar ta-baci a jiha, sashe na 305 (6) na kundin tsarin mulki yana bukatar rinjaye na kashi biyu bisa uku na kowanne majalisar domin shugaban kasa ya sanar ko tsawaita dokar ta-baci a jiha. Bisa samun gagarumin rinjaye, APC ka iya jagorantar majalisa na amincewa da irin wannan bukata cikin sauki, wanda ke ba shugaban kasa karin iko wajen harkokin tsaro na kasa ko rikice-rikicen siyasa.

Idan za a iya tunawa a lokacin muhawarorin da suka shafi ayyana dokar ta-baci a Jihar Ribas, majalisar dattawa ta fara dakatarwa saboda rashin samun yawan kuri’u kashi biyu bisa uku, yayin da majalisar wakilai ta amince da shi ne bayan cike ka’idojin aiki.

A yanzu APC na da ikon yanke hukunci a dukkan majalisun biyu, jam’iyyar mai mulki tana da damar zartar da muhimman hukunci bisa karancin bangaren ‘yan adawa.

A yayin da yake yin sharhi kan samun rinjayar jam’iyyar APC mai mulki da kuma ikonta a majalisar tarayya kafin zaben 2027, wani masanin siyasa, Farfesa Gbade Ojo, ya yi gargadi kan kalubalen da makomar dimokuradiyyar Nijeriya zai iya fuskanta.

“Abin da muke shaidawa shi ne, ci gaba da fadada jam’iyyar APC mai mulki. Duk da cewa hakan na iya bayyana a matsayin karfin siyasa a fili, tasirinsa ga dimokuradiyya abin damuwa ne sosai,” in ji shi.

Ya yi gargadin cewa a irin wannan yanayi, majalisar kasa na iya rasa ‘yancinta tare da zama ‘yar amshin shadar bangaren zartarwa. Ya ce idan har ‘yan adawa ba su tashi tsaye ba, to dimokuradiyyar Nijeriya za ta ci gaba da zama cikin hadari.

2027: Rikicin PDP Ya Kara Kazanta Yayin Da Aka Sake Samun Rarrabuwar Kai A Jam’iyyar

Jam’iyyar PDP ta sake fuskantar kazamin rikici bayan da babbar kotun tarayya a Abuja ta dakatar da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), daga amincewa da shirya babban taron jam’iyyar da aka shirya a Ibadan, Jihar Oyo.

Alkali James Omotosho ya bayar da umarnin hana wasu ayyuka yayin da yake yanke hukunci kan wani kara da ya kalubalanci halaccin taron da aka shirya, hukuncin dai ya sake sama tsofaffin raunuka jam’iyyar tare da janyo kazamin rarrabuwan kawuna a cikin babban jam’iyyar adawar ta Nijeriya.

Duk da hukuncin, shugabannin PDP sun dage cewa taron zai gudana kamar yadda aka tsara, suna bayyana hukuncin a matsayin cin fuska ga dimokuradiyya ta cikin gida da kuma tauye hakkin kundin tsarin mulkinsu na gudanar da harkokinsu na jam’iyya.

A cikin martanin kwamitin gudanarwa na kasa na jam’iyyar, ya sanar da dakatar da manyan jami’ai, ciki har da sakataren jam’iyyar na kasa, Samuel Anyanwu da sakataren shirye-shiryenta na kasa, Umar Bature da mashawarcin shari’a na kasa, Kamaldeen Ajibade da mataimakin mashawarcin shari’a na kasa, Okechukwu Osuoha saboda zargin karya kundin tsarin jam’iyyar.

Amma lamarin ya dauki sabon salo lokacin da wani bangare na jam’iyyar ya fitar da nasa jerin sunayen wadanda ya dakatar, wannan karon yana nufin shugaban jam’iyyar na kasa, Umar Damagum da sakatar yada labarai, Debo Ologunagba da wasu mutum hudu duk an dakatar da su, wanda lamarin ya kara rikitarwa game da wanda yake da cikakken iko a cikin PDP.

Wasu majiyoyi daga cikin PDP sun nuna cewa hana tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido, takarar shugabancin jam’iyyar na daya daga cikin musabbabin sabon rikicin.

“Lamido yana daya daga cikin wadanda suka ki shiga ayyukan PDP a baya har sai an dakatar da Wike. Yanzu an gan shi yana hada kai da masu goyon bayan Wike, wanda ke nuna inda sababbin rikicin ya sake kunno kai,” in ji wata majiya.

A cewar wata majiya ta daban, yunkurin Lamido na sayen fam din takarar shugaban jam’iyyar a makare wata alama ce na cewa akwai lauje cikin nadi.

“Ana sayar da fam a Gidan Legacy, ba a Wadata Plaza ba. An fara sayar da fam din ne tun a ranar 2 ga Satumba kuma an rufe a ranar 22 ga Satumba, tare da kara lokacin mika fam din har zuwa 27 ga Oktoba. To ta yaya mutum zai iya zuwa a ranar karshe ya yi ikirarin cewa bai samu fam ba?” in ji majiyar.

Yayin da PDP ke fama da shari’o’I a kotu, dakatar da juna da kuma tawaye na rarrabuwar kai, masu ruwa da tsaki a jam’iyya suna cewa babban kalubale yanzu shi ne sake gina sahihancin jam’iyyar da hadin kai kafin 2027.

Manyan jiga-jigan jam’iyya sun yi gargadin cewa idan ba a samu sulhu da jagoranci mai kyau ba, jam’iyyar adawa na iya fuskantar karin rarrabuwan kawuna kafin zaben 2027.

Ga jam’iyyar adawa mafi shahara a Nijeriya ta PDP, a halin yanzu aikin ya wuce kawai shirya babban taro, yana da alaka da dawo da aminci da hadin kai da kuma karfafa alaka kafin zaben 2027.

APC
Yusuf Shuaibu
+ postsBio
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027:Kamun Ludayin Yakin Neman Zaben Manyan ‘Yan Takarar Shugaban Kasa

MASU ALAKA

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
Tambarin Dimokuradiyya

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe

September 5, 2026
Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
Tambarin Dimokuradiyya

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta

September 4, 2026
Ko INEC Na Da Hannu A Rikice-rikicen Jam’iyyun Siyasa A Nijeriya?
Tambarin Dimokuradiyya

INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027

August 28, 2026
Next Post
Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku 

Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku 

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar da Shirin Ƙara Kuɗin Jarabawar WAEC da NECO

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

September 10, 2026
Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

September 10, 2026
Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

September 10, 2026
Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

September 10, 2026
Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

September 10, 2026
Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

September 10, 2026
Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

September 10, 2026
APC

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

September 10, 2026
APC

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.